A daren jiya ne fitacciyar mujallar nan ta bukukuwa da kwalliya da ake bugawa wata-wata da Turanci mai suna Tozali za ta karrama Adam A. Zango a wani gagarumin biki da za a yi a Abuja.
Za a ba jarumin kyautar Gwarzon Jarumi (Best Actor) a bikin wanda za a yi a katafaren wurin taro na International Conference Centre.
Inda cikin ikon Allah ya Lashe wannan kyautar muna tayaka murna a bisa wannan cancartar da kayi. Haka kuma mujallar Fim ta gano cewa za a karrama daya daga cikin jarumai mata guda uku da kyautar Jarumar Jarumai (Best Actress). Jaruman su ne Jamila Nagudu, Hadiza Gabon da Rahama Sadau.
Inda Jaruma Jamila Nagudu tayi nasarar Lashe wannan Kambu tsakanin Hadiza Gabon da Rahama sadau muna tayaki murnan abisa abin farin cikin nan.
A an karrama wasu manyan mutane da su ka hada da gwamnoni da ‘yan majalisa da ‘yan kasuwa, kuma an karrama wasu mata masu sana’o’i da kuma masu taimakon jama’a.
Title :
Photos: Adam A Zango Da Jamila Nagudu Sun Lashe Kambun Jaruntaka
Description : A daren jiya ne fitacciyar mujallar nan ta bukukuwa da kwalliya da ake bugawa wata-wata da Turanci mai suna Tozali za ta karrama Adam A. Za...
Rating :
5