Kwankwaso Ya Nemi Gafarar Kanawa.
Shugaban kungiyar hannun karba hannun rikewa Sharu Umar Gwammaja ya nemi gafarar Kanawa sakamakon tsayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin jihar Kano da Kwankwaso ya yi. Gwammaja yayi wannan furuci ne a yayin bikin cikar zagayowar ranar haihuwar tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso shekaru 60. " A baya mun yi wa Ganduje tayin Naira Miliyan Ɗaya domin cire jar hula, amma ya ki amincewa. Don haka yanzu mun ba shi awa 48 ya cire jar hula ko mu maka shi a kotu. Tun da dai ya sauka daga kan akidar Kwankwasiyya. Kuma muna neman afuwar Kanawa na kawo Ganduje da muka yi. Mun yi nadamar wannan aiki namu, amma a yayin zabe na gaba za mu sauya shi da wani. Muna fatan za a karbi tuban mu".
Title :
Na Tuba Ku Yafe Min Kuskuren Kawo Ganduje Da Na Yi - Kwankwaso
Description : Kwankwaso Ya Nemi Gafarar Kanawa. Shugaban kungiyar hannun karba hannun rikewa Sharu Umar Gwammaja ya nemi gafarar Kanawa sakamakon tsayar ...
Rating :
5