Tayi murmushi. Deena ta fito Antin nata
tace, "ke baki ga bako bane?" Ta
dubeshi tace, "sannu ko," tana hararar
sa ta kasan ido.Sam a ganinta ba
karamar tabewa bane ace kamar Antin nata ta aureshi. Deena ta shiga cikin
gida a fusace, anan ta samu Saif da Arfat
kannenta, suna ganinta suka taho da
gudu "Ya Deena" ta rungumesu tana
tausayin rayuwarsu tana tsoron halin
mahaifiyarsu, dolene Antinsu tayi auren da wannan kwashe kwashen da take,
tasan ita ba zata hana mahaifiyarta yin
aure ba, to amma Bilal bai kamata ace
shine zabinta ba domin yayi yarinta da
yawa duk da cewar ita tana da shekaru
28 tabbas za'a samu mai shekarunta a 'yan matan zamani. Shi yasa sam bata
so ta nuna Dina tace 'yarta ce, wai don
kar ace ta tsufa. Sam bata son raba
'ya'yanta a jiki shi yasa bata amince
suce mata Umma ko Mama ba sai dai
suce mata Anti. Arfat tace, ya Deena ina ice cream dina?
Tace na manta su a motar Anti bari naji
na dauko. Fitarta keda wuya taga yadda
yaron ya kanainaye a jikin Anty,
rayuwarta ta jagule zuciyarta tayi baki
taji ta tsani Bilal tamkar ta kashe shi take ji. Hankalin ta ya tashi ta raina
wayon Antyn tata, kasa karasawa wurin
tayi ta dawo cikin gida.
Bilal Idris wani matashi ne mai matukar
alfahari da baiwar kyau da Allah ya
bashi, yarone karami dan shekaru 22, dan Unguwar K/dan agundi. Asalinsa
buzaye ne, dan gidan buzaye ake cewa
gidansu. Ba masu arziki bane, anyi
ittifakin duk zuri'arsu talakawa ne sai
dai akwai su da son masu arziki, duk
inda mai mai yake to suna like da shi. Ya hadu da Karima ne awani dinner
daya yiwa abokansa rakiya. Da farko
Deena ya gani 'yar matashiya da ita ta
bashi sha'awa domin duk jama'ar dake
wurin shifa bai ga mai kyawun Deena
ba. Yayi tunanin yasa kai da dadin bakinsa ya koyar da ita soyayya irin
wacce yake ganin itace wayewa, domin
idan ya aureta lallai ya san kila
mahaifinta ya samar masa da abinyi,
kila su jawoshi a jiki ya shiga cikin
dukiya yayi kane-kane domin yayi auren jari, sai dai ko kallo Deena bai isheta ba.
Ya fita waje sukayi karo da Karima ya
sume a tsaye don kyawunta yaji shi bai
san ana samun mace mai haduwarta ba,
don shi yayi zaton budurwa ce na
tabbata ba mai ganin Karima yace ta taba aure kuma tana da 'ya'ya har 3,
lallai zawarawan zamani ba'a banbance
su da 'yan mata. Ya dubeta yana kashe
ido yace sannu, ta dube shi a yatsine
tace yauwa, yace naga kina zaune ke
kadai nazo na tayaki hira, tayi far da ido tace bana bukata nafison kadaici.Ya
sake gyara zama cikin harshensa na
mayaudaran maza yace, "A tunani na
duk mutum mai tunani mai hankali ba
zai taba son zama shi daya ba, dalili na
shine zama cikin kadaici na sa damuwa da yawan tunani, hakan zai sanya
mutum hawan jini ko bugun zuciya".
Tace ka gani mutum mai yawan
magana bai cika burgeni ba, haka na
tsani mutum mai shish-shigi, yayi
murmushi hade da kashe ido da wani likimo duk na yaudara kamar yadda aka
fi sanin mayaudaran maza nayi yace,
Baby kinsan kina da kyau? Gaskiya koki
yarda ko kar ki yarda na kamu da son ki,
zan iya rasa rayuwata ne duk lokacin da
bakinki ya furta Bilal bana son ka. A tsanake ta mike tana wani irin taku
wanda aka fi samunsa a gurin duk mace
mai budadden ido da wayewa. Bilal ya
bita da kallo saboda yadda ta tafi da
hankalinsa, ta shiga cikin hall din da ake
party, ta shiga a dai-dai don amarya da ango ne ke casu, ita ma ta shiga ta taka.
Deena na gefe na ganin yadda Anty ta
ke chashewa alhali ga wasu na lika
mata dollas, hankalinta yayi kololuwar
tashi, har ga Allah Deena bata son zuwa
irin wadannan gurin takan zo ne saboda ta san dole Anty zata ki yin wani abu
idan har tana gurin. Lokacin da aka
tashi daga dinner, Bilal bai hakura ba ya
nace mata yace, baby zaki tafi baki bani
lambarki ba, sannan kuma baki saurare
ni ba, yayi kalar tausayi yace ''idan kika yi haka zaki tafi ne ki barni cikin rudu da
tunani, hakika zuciyata tana sonki. Lallai
yau idaniyata zata kasa bacci zata tsaya
cak da aiki. Lallai yau idan na barki zan
bakunci lahira domin rayuwata na cikin
hadari''. Zuciyarta ta buga dam, domin ba abinda takeso face tattali da anuna
mata soyayya, duk kuwa da cewa babu
tattalin da ba'a nuna mata abaya ba
wurin tsohon mijinta. Hajiya. Karima ta
figi motarta, ita kuwa Deena ta
sunkuyar da kai bata ce komai ba. Bilal ya koma gida da tunani duk hanyar da
zaibi ya samu Ya ko Kanwar zai bi,
domin shi tunanin shi Deena kanwar
Karima ce. Hakika duk yadda hatsabibin
matashi yakai Bilal yaje koma ya wuce
nan, domin shi a tarihin rayuwarsa babu abinda yake so tamkar mace, mayen
mata ne kuma bai taba cewa yanaso
ance ba'a sonsa ba, domin duk yanda
zan kaiku ga kwatanta muku yadda
Allah ya tsara halittar Bilal abin ya fi
gaban nan 'ya'yan manya dasu yake soyayya, sai ya gama lalube yarinya zai
gudu, dan Bilal bai san iya adadin 'yan
matan da ya taba ba.Ko da ya koma
gida sai rayuwarsa ta jagule yanason ya
tuna fuskar Deena, tsarinta ya burgeshi,
to ya zai yi gashi ya furtawa Yar? amma ko Yar ya samu zai yi maleji idan bukata
ta biya ya yi gaba abinsa bashi kenan
ba?.
Tarkon so mai wuyar ciruwa, hakika yau
ya kama Karima a makogwaro domin
kalaman Bilal take ji, komai nasa ya yi mata, matashi kosash-she, lallai irinsa
ne zabinta, ai da ta sani ta bashi card
din ta, sai taga kai gwanda ta garashi
dan ita tana son taga ana irin riritata
din nan hakan ya sa ta shariya. Bilal sai
da ya samu adireshin din Karima har lambar wayarta ta hannun kawarta
kubra.
"