MUGUN MIJI
PART (1)
.
___________NA_______
ZAHARA'U BABA YAKASAI
. A hankali take tukin motar ta end of
discussion green kala ta fito daga
number one city da ke titin IBB
way,kyakkyawar mace ce wacce ta amsa
sunan haduwa,hajiya Kareema gefen, ta
yar matashiyar budurwa ce sanye da doguwar riga da Hijab dinta, Deena ta
juyo ta kalli hajiya tace, "Anti ki aje ni a
koki ko?'' Hajiya Kareema ta bata ranta,
tayi kicin-kicin tace, "ba zan aje ki ba,ni
ban ga dalilin da kike fifita duk wanda
ya danganci ubanki a kaina ba'' Deena ta sunkuyar ta kanta tana kallon
yatsunta,tana mamakin mahaifiyarta da
irin halinta. Ta gyada kai ta fito da
furucin mahaifinta da yake yawan
fadawa mahaifiyar tata, ''duniya zata
koya miki hankali,domin na kula ke ba ki san komai ba a babin rayuwa ba''.
Tabbas ita ma Deena kallon da take
yiwa mahaifiyar tata kenan,ko yaushe
ne duniyar zata koyar da Anti darasi?
oho! Haka sukayi shiru babu wanda ya
tankawa wani sai can wayar kareema ta soma kida,ta sanya hannu ta dauka
yadda take kashe murya ya sanya Deena
kwanciya jikin kujerar tana jin wani
azababben takaicin mahaifiyar ta. ''Baby
na ka iso?'' ta fada tana kashe
murya.can tace,''ganinan zuwa, ka bani minti goma zan iso''. Ta kashe wayar,
Deena ta kasa hadiye takaicinta, ta ce
Anty waye yazo,bako kika yi?'' ta kada
kai tace , Bilal ne'' fuskar Deena ta
daure tam, ta ce Anty Bilal fa karamin
yaro ne,nifa ina gaya miki yayi miki kankanta ki aure shi kin girme shi fa''.Ta
dakawa Deena tsawa tace ''so kike na
auri tsoho? An gaya miki ni din wata
babba ce banda kaddarar haihuwarku ai
kin san ban isa na haife ku ba,kuma da
kike cewa na girme shi, ai nana khadija ta girmewa manzon Allah S.A.W .
saboda haka kinga ai nayi sunna ko?
Deena tace,''tafsirai da yawa sun nuna
nana khadija bata girmi manzo Allah
S.A.W ba, sai dai ana ganin yana
shekaru ashirin da biyar ita ma tana da ashirin da biyar suka yi aure.mafiya
yawan malamai sun yarda da hakan. Ta
daka mata tsawa, ''rufe min baki, zan
haife ki a cikina a ce kin fini sanin
duniya ne,ko kin fini hankali. Bilal shine
mutumin da naga ya dace da ni,shi ne wanda zan aura,kuma ke baki isa ki
hana ni jin dadin rayuwata ba, Ita kam
Deena tayi shiru bata ce komai ba,tana
mamakin budurwan zuciya irin ta
mahaifiyar ta. Haka suka isa gida,wani
makeken gida ne wanda samun irinsa da haduwarsa na da wuya.cikin G.R.A
gidan yake ko a can din ma gidan yana
daga jerin gidajen da samunsu a gurin
ba karamin abin alfahari bane.Mai gadi
ya bude kofa tayi fakin Bilal cikin wasu
kananan kaya ya fito, yaro ne kyakkyawa ajin karshe a kyau.ya hadu
matuka fari ne sol,gashin kansa a
kwance yake tamkar gashin mutanen
hindu.Gashi ya dauki gyara na
zamani,ya iya daukar kwalliya domin
komai hassadarka Bilal yayi. A hankali ya ringa taku ya bude mata kofa yana
wani irin murmushin burgewa yana
kallonta tsakiyar ido irin kallon da maza
'yan duniya ke yiwa wayayyun mata.
"My Dear kin shanyani fa,"
Tace, "haba Baby na muna hanya ne amma yanzu gani na iso, ai bansan zaka
zo ba dama ban fita ba."
Yace, "ina gida kawai naji inaso in
ganki, ni kuma idan ban ganki ba
bazanji dadin rayuwata ba,
". Pls comment after read