Ko ma menene ya faru ,shegen kwad'ayi na ne ya jaza min daga yin
mafarkin ina cin tsiren hanta da madara ,na kwaso kafa na taho gidannan
wajen mijina amsar d'ari biyu[farkon labarin],ga irinta nan,domin wannan
zuwan ne ya zamo silar faruwar komai',maganar meera da take cewa'sister
kama mukai kayan d'aki!', ya zamo silar katsewar tunanin hibbatu!
Cicci6ar kayan sukayi tare da nufar d'akin da ammi ta tare,bayan sun
ajje kayan,suna sauke numfashi,tare da tsayawa suna masu 'karewa d'akin
kallo,ammi suka hango a tsakiyar gado lullu6e da wani had'ad'd'en
mayafi,kamar wata budurwar amarya,galala suka tsaya dubanta sannan suka
dubi junansu,suka sauke ajiyar zuciya!
Hajiya ce ta shigo d'akin cikin shiga na alfarma da kwalliya wato
shiryowa taje tayi,dubansu tayi tace 'da ku za'a sayi bakin ammin
naku...' ,sallamar alhaji da bilal ne ya katse maganar hajiya,hajiya ta
amsa tare da cewa 'barka da shigowa ango mijin amarya' ,murmushi alhaji
yayi yace 'yawwa uwargida ran gida' ,yana mai kokarin zama akan gado
kusa da ammi take,hajiya ta dubeshi tace 'ango yana ga kana kokarin zama
ba tare da munyi cinikin siyan bakin amaryar taka ba',bilal ne yayi
caraf yace mata 'umma ungo,ni da kaina zan siya masa bakin amaryarsa'
,ya mi'ka mata bandir d'in 500,tare da mi'ka mata kuma ba'kar
leda,sannan yayi gyaran murya ya kwararo addu'a,alhaji da hajiya sai
zabga 'amin' suke,bayan sun shafa ne,bilal ya dubesu yace'toh ni zan
tafi alhaji,ALLAH yasa mu a danshinku' ,alhaji yana washe baki yace
'amin bilal,kai ma war haka wani satin za'a kawo maka amaryarka'
,hibbatu da meera wanda babu mai bi takansu ,domin yadda suka gama
'kamewa kamar rigar da akayiwa starch,yasa zaka zata basa d'akin
,furucin alhaji ne yasa hibbatu tayi wuf tace'wacce amarya kuma,akwai
amaryar da ta wuce ameera' ,meera tace 'gaya masu dai sister,daga kan mu
babu vacancy',bilal dariya ce ta taho mai amma sai ya gimtseta yana
cewa 'abba sai da safe' ,hibbatu tayi caraf ta ri'kewa bilal hannu tana
ja tace 'habibi da'iman dan Allah taho mu tafi gidanmu',meera ita ma
hannu tasa tana turashi tace 'wuce muje my blood,daka kaina babu
'kari,kana damu ,kuma ake maka zancen amarya' ,a haka dai suka fice,suka
bar hajiya da alhaji da yin dariya,ita kanta ammi sai da ta dara!
Bilal yana yin parking ,hibbatu da meera suka fito daga motar,yana bud'e
masu gidan suka afka ciki a guje,yanayin gidan ya burgesu,gaskiya
alhaji yayi kokari,ba tare da 'bata lokaci ba ko wacce ta fad'a d'akinta
,da yake kowa ya san kalar kayan d'akinsa,wanka da kwalliya suka
feso,suka fito hibbatu ta shiga kitchen bayan ta bawa meera umarnin taje
ta kula da bilal ta kuma tabbatar tayi masa wanka !
Misalin 9:00pm ,suna zaune a tsakiyar falon ana kwasar girkin da hibbatu
tayi daga shigowarsu d'azu [sunji batun amarya ,hibbatu ta dawo
hankalinta]
suna gama cinyewa ,meera ta kwashe plate ta kai kitchen ta dawo ta zauna
,bilal ya dubesu yayi murmushi yace 'matana abin alfaharina,anya a
duniya akwai namijin da ya kaini gata',murmushi kawai sukayi suna masa
tausa,nan dai ya had'asu yayi masu fad'a da nasiha ,sannan ya dubi
hibbatu yana cewa 'sai ki tsara kwana nawa nawa zan dinga yi a d'akin
kowaccenku' 'kwana d'aya' hibbatu ta bada amsa ta cigaba da cewa'idan
kagama yin kwana bakwai a d'akin ameera,toh kwana d'aya zaka dawo ka
d'inga yiwa ko waccen mu ,girki kuma kullum tare zamu d'inga yi da
ita,mu had'u mu uku muci,da dare kuma ,mai miji ta wuce d'aki da
abunta,ko ya kike ce ameera' ,meera tace 'hakan yayi wallahi,ni daman na
tsani inga ana raba tukunya a gida d'aya bilal yace 'toh shikenan Allah
ya bani ikon yin adalci a tsakaninku ' 'amin' suka amsa,hibbatu ta
mi'ke ta janyo ledar dake kusa dashi ta ciro kaza d'aya tana cewa 'toh
ni sai da safenku ',sannan ta ballo cinyar kazar ta kai baki ta yagi
tsoka tare da mur'kushewa ta wuce d'aki tana taunar tsokar tana lumshe
ido dan dad'i,hannunta ri'ke da sauran gangar jikin kazar....
Hibbatu tana shigewa d'aki ta janyo wayarta ta bugawa imad tana
tambayarsa ko yasan cewa ammi ta auri abba ,dariya yayi yace'bilal ya
fad'a min,kuma nayi masu murna,ke ma ya kamata ke da meera ku dawo gidan
aurenku ku zauna' ,'tun yaushe muka dawo imad,ALLAH ya bamu juriya da
hakurin zama da juna' 'amin' ,'ka gaida matar taka bye' ,imad ya amsa da
'za taji,take care!',suna gama waya ,hibbatu ta cigaba da ragargazar
kazarta tana rausaya kanta
* * *
Washegari alhaji ya bugawa bilal waya akan cewa yana son ganinsu gaba d'aya!
Misalin 10:00am falon gidan alh.salis goni cike yake da matansa umma da
ammi,sai kuma bilal da matansa hibbatu da meera,alhaji yayi gyaran murya
ya fara kwararo addu'a ,sannan yayi masu nasiha ,ita ma hajiya tayi
musu fad'a tare da cewa 'ku had'e kanku ku kauda fitina a zamanku,domin a
cikin mu babu mai bin bayan ko waccenku a duk lokacin da ta kwa'be
muku' ,ammi tace 'ahtoh,kuji da gidan mijin ku,muma muji da namu gidan
mijin,kuma kada ku kuskura ku shanya borkono ballantana ku sa ran daka
yaji' ,hibbatu jiki yayi sanyi kalau ,daman ita ta d'ora akai,meera bata
d'auka da zafi ba,domin ita kawai burinta ta zamo mata ga bilal,bayan
an gama masu fad'a da nasiha,alhaji ya basu umarnin tafiya bayan ya
dam'kawa hibbatu da meera mu'kullin mota!
¤BAYAN WATA ASHIRIN BIYU¤
Hibbatu da meera zaune akan keken guragu ,nurses suna turasu za'a shigar
dasu d'akin haihuwa da ke cikin asibitin 'kasar cairo ,sai faman ihu
suke suna kururuwa,larabawan da ke gun sai kallonsu ake gwanin
sha'awa,hibbatu hannunta dam'ke da rigar bilal tana cewa 'mugu
kawai,daga yau kai zaka d'inga d'aukan juna biyun,ka haihu in yi
raino',meera kuwa idan azaba nakud'ar ta ciwo ta ,sai kama cinyarsa ta
mintsineshi,bilal kuwa dake tsakiyarsu ana turasu ,hakuri yake basu da
musu sannu ,duk yabi ya rud'e,haka aka shige da su d'akin haihuwar,shi
ko yana waje yana safa da marwa tare da zuba addu'a,bayan awa biyu nurse
ta fito ta sanar bilal cewa duk sun haihu kuma ansamu baby boys,sujjada
bilal yayi domin nuna godiyarsa ga Allah,a take ya ciro waya ya buga
gida nigeria ya sanarwa dasu alhaji ,bayan angama kimtsa hibbatu,meera
da jariransu,aka maidasu d'akin hutu,domin su kwanta su huta,bilal ya
shiga yana masu murmushi tare da musu sannu,hararar wasa suka masa,gun
jariran ya nufa, suna kwance a 'kananun gadajensu, kallonsu yake yana
hawaye,yayi musu hud'uba da shoaib da khamis,wayarsa ya d'auko ya
d'aukesu hoto,ya turawa su alhaji da imad ta whatsapp,wata balarabiya
mace aka shigo da ita ta haifi yan biyu ,d'aya gadon dake kusa da nasu
meera aka kwantar da ita da jariranta,wani ne ya shigo da murnarsa ya
nufeta daga ganinsa kasan mijinta ne,hibbatu ce ta dubesu cikin harshen
larabci tace 'na maka murna affan,the babies are cute' ,da mamaki affan
ya dubeta yace 'hibba what a suprise',ya mi'kawa bilal hannu sukayi
musabaha,hira akan jariransu ta 'bar'ke tsakaninsu duka,shigowar wata
nurse ne ya katse hirar tasu,gun bilal tazo tana kwarkwasa ta mi'ka masa
discharging letter tana kashe masa eyes,hibbatu ta duro daga kan gado
,ta wafci takardar tana cewa 'duk kiyi ki gama iskancinki,mijin mu dai
ba aro ba d'ani ,tsakaninki dashi sai dai kallo da maida mugun yawu '
meera itama ta duro,ta sungumi abbu da abba ta dubi bilal tana cewa 'my
blood lets go home' sannan ta dubi hibbatu tace'sister gaya mata dai da
manyan ba'ki,kuma ta kwana da sanin cewa bilal mijinmu ne mu kad'ai ba
MIJIN HAYA ba....!
[tammat bhi hamdulillah]
anan nakawo 'karshen labarin MIJIN HAYA,all thanks 2 Allah for making it possible!