Meera ta cigaba da bawa hibbatu baki ,tare da lallashinta,har ta samu hibbatu ta ci abincin...
* * *
Washegari ! misalin 'karfe 6:00am,ammi tana zauna tana lazimi,abbu ya
bud'e idanunsa yana mai sauke ajiyar zuciya tare da yin salati,ammi ce
ta matsa gareshi tana masa sannu,duk yabi ya fita hayyacinsa kamar wanda
ya shekara yana ciwo,duban ammi yayi,tare da bud'e bakinsa da 'kyar
yace 'bani ruwa na sha' ,ammi yatsa tasa ta danna emergency alert button
dake ma'kale a jikin bango d'akin,da hanzari nurse on duty ta shigo
d'akin ,ammi ta umarceta da ta kira doctor,patient d'insa ya farfad'o
,ba'a fi minti biyu ba, likita ya shigo,ya duba abbu ,ya kuma umarci
ammi ta had'a masa tea ya sha,ta kuma bashi maganinsa,cox in the next
1hour za'a shiga dashi theatre domin a cire masa 'kodarsa da ta lalace
kafin ayi undergoing final stage of the surgery'
Bayan ammi ta gama yi masa komai kamar yadda likita ya umarceta,sai abbu
ya dubeta bayan ta gyara masa kwanciya yace 'wai meye same ni ne,naji
likita yace za'a cire mini lalatacciyar kod'ata a dasa min wata,yi min
bayani' ,ammi ta gyara zama ta fara labarta masa abinda ya faru tun
bayan sumewarsa a jiya, har izuwa yanzu da yake kwance rai a hannun
Allah,'mtcsheeew!' dogon tsaki abbu ya ja yana cewa 'don wulakanci a
rasa 'kodar da za'a dasa mini,sai na wannan d'an iskan yaron,salon kuma
ya goranta mini inna warke ko?' galala! ammi ta tsaya kallon abbu domin
ya mugun bata mamaki ,ya cigaba da cewa 'idan yarana sun 'ki bada
kodarsu guda d'aya a dasa min,ke da kike matata me zai hana ki bada taki
a dasamin' ,ammi tayi caraf tace 'wa? Ni asuwa? ,'ya'yan cikinka basu
bada nasu ba,sai ni dana ke yar d'orin d'osono ,matarka,in har bazaka
amince a dasa maka 'kodar bilal ba,i shikenan sai ka jira mutuwarka'
abbu ya kuma jan tsaki ,a kasaushe yace 'a rasa 'kodar da za'a dasa min
sai 'kodar mutumin dana fi tsana a rayuwata,gwara in mutu da akan in
rayu da 'kodar yaronnan a jikina' karaf a kunnen su hibbatu da suka
shigo d'akin ita dasu alhaji da meera,hibbatu tayi caraf tace 'ta fi
nono fari,daman ba lallai babu dole zama da uwar kishiya,ni ma ba'a son
raina naso bilal ya bada 'kodarsa ba,ALLAH UBANGIJI YA JIKANKA YA KUMA
YAFE MAKA KURAKURANKA,SHI KUMA BILAL ALLAH YA BASHI LADAN NIYYA'..da
'AMIN!' meera,hajiya da ammi suka amsa....
Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee isma'il MIJIN HAYA [62]
na ILILEE
Alhaji ransa a matu'kar 6ace ya dubi ammi yace 'ki taso muje mu amso
masa discharging letter,tunda hakan ya za6a wa kansa' ,ammi ta taso tana
goge idanunta da gefen hijab d'inta,su ka fice gaba d'ayansu suka nufi
ofis d'in likita ,kici6us sukayi da bilal da imad wanda sai yanzu suka
dawo daga masallaci,bilal ya russuna ya gaishe da alhaji da
hajiya,sannan ya dubi ammi yana tambayarta ya jikin abbu ,'ka je ka
ganewa idanunka' ammi ta bawa bilal amsa,da hanzari bilal ya tashi ya
nufi d'akin da abbu yake,imad yana kokarin bin bayansa, hibbatu ta
tareshi tace 'kyaleshi yaje shi kad'ai,'kila hakan ya zamo sanadiyar da
zai gane cewa abbu ba zai ta6a kaunarsa ba' ,imad a firgice yace'abbun
ya farfad'o ne?' 'eh' ammi ta bashi amsa,ta kuma labarta masa yadda suka
kaya dashi ,alhaji ya d'ora da cewa 'yanzu haka dischargn letter zamu
amso masa' ,imad ya jinjina lamarin a zuciyarsa yana mai mamakin halin
abbu,'amma fa ba abin mamaki bane,domin abbu zai iya yin fiye da haka'
zuciyarsa ta tunasar dashi
Bilal ya tura 'kofar ya shiga da sallama,a zuci abbu ya amsa sallamar
yana mai duban bilal da idanunsa da sukayi mici mici,umarni! abbu ya
bawa bilal da ya sawa 'kofar lock,bayan bilal ya aikata hakan ,ya
'karaso kusa da gadon abbu yana mai rusunnuwa tare da yi masa ya
jiki,abbu murmushi yayi yace masa 'zo kusa dani ka zauna d'ana,tashi ka
zauna' ,tamkar a mafarki bilal ya ji maganar abbu ,sai da abbu ya 'kara
yi masa magana,sannan ya mi'ke ya zauna a kunyace kusa da abbu ,abbu ya
kamo hannun bilal yace 'd'ana,ALLAH yayi maka albarka' sannan ya cigaba
da cewa'tabbas da amminsu imad ta labarta mini abinda ya faru jiya da
kuka kawo ni asibiti,naji kunya matu'ka hakan yasa na nad'e tabarmar
kunyata da hauka,saboda i dnt deserve ur kidney,bilal ban cancanci ka
bani kod'arka ba,domin ni azzalumi ne,na yi maka tabo a rayuwa,na tauye
ka,na zalunce ka,bilal i don't deserve your sympathy at all,kaico na,na
tafka kuskure babba a rayuwata,na raba d'an uwana da mahaifarsa da
danginsa, saboda kwad'ayin dukiya da kuma ba'kin kishi irin nawa,kuma
ALLAH yayi ikonsa ya cusawa y'ata soyayyar d'ansa a zuciyarta,wallahi
wannan ishara ce babba a gareni,domin daga farkawata zuwa yanzu na gano
cewa bawa ba a bakin komai yake ba ,ji yadda na koma ,dubeni bilal,ina
dukiyai,iina bokon ,ina prestige da attraction danake seeking for,duk ba
za su bini kabarina ba bilal,a yanzu yafiyarka kawai nake bu'kata domin
shine zai zamo mini babban waraka a gareni ' bilal da tuni ya soma kuka
yace'abbu na yafe maka tun a jiya wallahi,cause everything happens for a
reason',malalacin murmushi abbu yayi tare da rungume bilal yana cewa
'jazakallahu khairan ya bilal',bugun kofar da akeyi ne yasa bilal ya
tashi yaje ya bud'e,likita ne dasu alhaji!
Ganin bilal na goge hawaye daga idanunsa,yasa hibbatu da meera suka
hanzarta kama hannunsa suna tambayar sa lafiya ,ammi kuwa cewa take
'kaji da kunnenka yanzu, sai ka hakura da batun bada 'kodar taka a dasa
masa'
likita ne ya 'karasa kusa da abbu yana cewa 'haba patient meyasa bakaso
ayi maka kidney transplant?,abbu yace 'pls kace masu su matso kusa ina
son magana dasu',likita zai yi magana .abbu ya katseshi yace 'just call
them' ,likita yacewa su alhaji su matso abbu yana son musu magana..!
Abbu ya kama hannun hibbatu da imad yana cewa'ban yi bakin ciki ba dan
kun 'ki bada 'kodar ku a dasa min ,coz nasan i was'nt a good father to
u,especially hibbatullah nasan na zalunceki bt pls ki yafe mini' hibbatu
ta fashe da kuka domin kalaman abbu sun yi kama da wasiyya,ganin yadda
yake magana da 'kyar yasa tace 'abbu na yafe maka wallahi,nima ka yafe
mini' imad yace' pls abbu kayi shiru haka,kasan baka da lafia',abbu tari
yayi ya cigaba da cewa 'na yafe miki ya bint ,ga bilal nan,ku d'aukeshi
a matsayin uba',ya kuma yin tari ya dubi alhaji yace'my friend,pls ga
amanar zuri'ata nan,kuma ina son ka had'a kan dukiyata ka dam'kawa
bilal,bcoz he's the rightful owner' alhaji kuka kawai yake ya kasa
amsawa,abbu ya dubi ammi yace 'matata matso kusa dani' ,matsowa tayi ,ya
kamo ta ya rungume su duka tare da imad da hibbatu yace'ALLAH YAYI MUKU
ALBARKA',yana rungume da su ya yafito bilal da hannunsa,shi ma ya
matso,ya had'a dashi ya rungumesu yana cewa 'i love you all' ,ya dubi
meera da hajiya yayi masu murmushi a hankali yace musu 'ku yafe min '
,murmushi mai d'auke da hawaye ne ya subce masu ,hajiya tace 'ALLAH YA
YAFE MANA GABA 'DAYA' ,meera da alhaji sukace 'amin',abbu ya lumshe
idanunsa yana mai cewa 'astagafirullah!' a zuciyarsa!
Sanyin da jikin abbu yayi ne yasa imad,bilal,ammi da hibbatu da suke
rungume da jikinsa .suka farga da cewa ashe rai yayi halinsa,abbu ya
amsa kiran mahaliccinsa!..
Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee isma'il MIJIN HAYA [63]
na ILILEE
Likita ne ya 'kara tabbatar masu da mutuwar abbu bayan ya dubashi,kowa a
d'akin sai da jikinsa yayi sanyi,sai koke koke da addu'o'i suke
yi..,alhaji yayi clearing bill,aka had'a masu gawar abbu suka tafi da
ita!
Fadar mai martaba[usulin ammi] aka wuce da gawar abbu,anan aka masa
wanka,akayi masa sutura ,aka sallacesa aka sada shi da gidansa na
gaskiya!
BAYAN KWANA ASHIRIN!
Bilal,imad da alhaji suka d'aga zuwa 'kasar OMAN!
Bilal yaga gata ,so,da kulawa a gun danginsu da sukayi ragowa,domin ko
ba'a fad'a masu ,suna ganin fuskar bilal suka san cewa jinin khamis
ne,kuma sun koka da mutuwar Bilal yaga gata ,so,da kulawa a gun danginsu
da sukayi ragowa,domin ko ba'a fad'a masu ,suna ganin fuskar bilal suka
san cewa jinin khamis ne,kuma sun koka da mutuwar abbu!
Hibbatu tana tare da ammi a fada ,domin anan ake karbar gaisuwa da zaman
makoki,haka zalika meera tana tare da hibbatu,domin ita ce take bata
baki,hajiya kuwa kullum tana fada ,sai dare take komawa gida!
Ranar da akayi sadakar ar'ba'in ,a ranar meera ta tattara ta tafi gidansu,ta bar hibbatu a fada!
Alhaji ya cika alkawari ,domin duk wata kadara da dukiya ta abbu,ya had'e kanta ya dam'kawa bilal da imad!
Imad kuwa ya koma cyprus domin ya kamalla karatunsa!
*BAYAN WATA GOMA!*
bilal ya gaji da zama shi kad'ai a gidansa,kuma wai da sunan yana da
mata har biyu,ya je fada domin ya d'auko hibbatu ,hibbatu tasa masa kuka
wai tana nan tafe,pls zata dawo a duk sanda ta shirya,bilal ha'kura
yayi tare da yi mata uzuri ya kyaleta,hibbatu kuwa ,a 'kasan zuciyarta
bakomai ne ke d'awainiya da ita ba face kishi,domin idan ta tuna cewa
yanzu fa bilal ba Mijinta bane ita kad'ai sai taji sam sam bata sha'awar
komawa gidansa!
Meera itama cewa tayi bazata tare ba,sai hibbatu ta koma!
Bilal share su yayi duka biyun,ya watsar da lamarinsu, aikinsa kawai
yasa a gaba yana yi ,saboda still a goni motors yake aiki,dukiyarsa kuwa
masallatai da makarantu na marayu ya gina,kuma bai manta da dangin
mahaifiyarsa ba domin sai da ya bi kowannensu ya basu jari ,sannan yasa
aka rushe masu gidansu aka tada ginin zamani,sun ji kunya kuma sunyi
nadama matu'ka!
Imad ya kamalla karatunsa ,yazama cikakken consultant,makudan kud'i
bilal ya bashi domin ya gina asibitin kansa, 'kasar oman imad wuce ya
tamfatsa asibitin sa tare da yin settling down a can,ya kum samu
balarabiyar mata ,aka sha bikinsu ya tare da amaryarsa!
Hajiya da kanta ta wanke 'kafa ta tafi fada domin dawo da hibbatu
d'akinta,domin hakan kad'ai zaisa ita ma meera ta tare,fafur hibbatu
tace bata shirya komawa ba,daman itama ammi ta gaji da lallashinta
,domin tayi masifar duk a banza,shiyasa ta xuba mata ido,saboda shi
kanshi bilal yace 'a kyaleta kawai',hajiya ta hango tsagwaran kishi a
idanun hibbatu,hakan yasa ta yanke wata shawara a zuciyarta!
Alhaji taje ta sanarwa,shikuwa yace bashi da matsala,idan har wacca akayi shawaran akanta ta amince shikenan!
* * *
Direba ne ya sauke hajiya a fada,bangaren da ammi ke zaune a fada ta
nufa,bayan ta gaida matan gidan ta wuce d'akin ammi,bayan sun gama
gaisawa,hajiya ta dubi ammi tace 'ammin imad magana ce mai muhimmanci
zamuyi,ina son ki kalli abin ta fuskar fahimta' ,ammi ta zuba mata idanu
tare da cewa 'ina sauraronki',hajiya tayi jim sannan tace 'ina son ki
auri abban ameera.....!'
Hakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IHakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL MIJIN HAYA {64}
na ILILEE
Ammi dariya tayi tare da cewa 'dan Allah da gaske kike ko wasa?' ,hajiya
ta amsa da 'wallahi babu batun wasa,domin aurenki da abban ameera ne
kad'ai zai sa hibbatu ta koma gidan bilal,kuma kasancewarmu abokan zama
zaisa suyi koyi da mu' ,ammi tayi jim sannan tace 'toh shi abban ameera
ya amince ne' ,'da sanin shi ma na taho gunki,amincewarki kawai muke
bu'kata ' hajiya ta fad'i tana mai duban ammi ,tana jiran amsa' ,ammi
tace'toh shikenan,ALLAH yasa wanda akayi dominsu ,su farga' ,'amin'
cewar hajiya ,nan suka cigaba da tattaunawa akan lamariAmmi dariya tayi
tare da cewa 'dan Allah da gaske kike ko wasa?' ,hajiya ta amsa da
'wallahi babu batun wasa,domin aurenki da abban ameera ne kad'ai zai sa
hibbatu ta koma gidan bilal,kuma kasancewarmu abokan zama zaisa suyi
koyi da mu' ,ammi tayi jim sannan tace 'toh shi abban ameera ya amince
ne' ,'da sanin shi ma na taho gunki,amincewarki kawai muke bu'kata '
hajiya ta fad'i tana mai duban ammi ,tana jiran amsa' ,ammi tace'toh
shikenan,ALLAH yasa wanda akayi dominsu ,su farga' ,'amin' cewar hajiya
,nan suka cigaba da tattaunawa akan lamarin!
*BAYAN KWANA 5*
Alhaji da kanshi tare da bilal su kaje fada,gun mai martaba neman auren
ammi,kuma alhaji ya zayyano masa hujjarsu na yin haka,a take mai martaba
ya umarci waziri da ya amshi sadaki liman kuma ya d'aura auran,kowa
dake zaune a gun suka shaida...
Duk wani shirye shirye hajiya ta gama yi,da kanta ta had'awa ammi lefe
da kuma kayan d'aki ta kuma dasa mata su a d'akin da zata tare,da yamma
direba ya kai ta fada domin ta d'auko ammi!
Hibbatu ganin ammi na had'a kaya cikin akwati, yasa tace 'ammi had'a
kayan me kike yi?' ,ammi ta cigaba da had'a kayanta tace 'gidan mijina
zan tafi' ,'gidan abbu?' ,'me zanje in yi a gidansa,d'azu da rana aka
d'aura min aure' ,hibbatu hannu akan kirji tace 'aure ammi? ,wanene
mijin,tafiya zakiyi ki barni' ,ammi ta amsa mata da cewa 'ki zauna
sanya,kuma ba tafiya zanyi in barki anan ba,ki shirya ki rakani gidan
mijina,daga nan ki wuce gidan ubanki,tunda gidan mijinki ya gagareki
komawa' ,shigowar hajiya ne ya katse maganar da sukeyi,hajiya tace
'ammin imad kin shirya mu wuce ' ,'eh' ammi ta bata amsa,barori ne suka
kai kayan ammi mota,hajiya da ammi suka shiga cikin gidan domin suyi
sallama da matan gidan....
Hibbatu da 'kyar taja jikinta ta bi su ammi!
Sun iso gidansu meera,maigadi ya wangale gate,direba ya danna hancin
mota ya shige,hajiya ta sauko daga motar hannunta ri'ke da na ammi suka
shiga cikin gidan bayan ta bawa direba umarnin shigo da kayan ammi,ita
dai hibbatu tana biye dasu kamar kazar da 'kwai ya fashewa a ciki,wani
d'aki taga sun shige,turus tayi ta tsaya a falo tana wani irin bahagon
lissafi,har direba ya gama shigo da kaya ya dire a falon,meera ce ta
fito daga d'akinta tana zuba mi'ka ,ganin hibbatu a tsaye kamar wata
gunki,yasa ta 'karaso tana cewa 'oyoyo sister' ,hajiya ce ta fito ta
dubesu tace'ku kwaso kayan amminku ,ku shigo dashi' ,hibbatu ce tayi
ya'ke tace 'hala ammi ta dawo gidannan da zama ne?',hajiya ta murmusa ta
bata amsa da 'ehmana,ta dawo gidannan da zaman aure' ,meera tuni ta
wartsake cike da mamaki tace 'aure?' ,'eh aure dai da kika sani' ,tuni
hibbatu da meera suka had'a bakunansu wajen jifan hajiya da tambayar
'wanene mijin ?' ,'abbanku!' ta basu amsa,mamakine 'karara ya bayyana a
kan fuskarsu ,musamman hibbatu data dafe cikinta dake faman 'kugi ,tace
'kina nufin ke da ammi kun zama kishiyoyi' ,hajiya tace 'ki gyara
zancenki,abokan zama zaki ce' ,nan ta wuce ta barsu anan bayan tace masu
'idan kungama jajantawa junanku,sai ku shigar wa da amminku kayanta
d'aki'..
Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee isma'il