Bilal idanunsa cike da 'kwalla ,ya dafe kansa yana mai karanta
'innalillahi wa inna ilaihi raji'un' ,meera tuni fuskarta ya gama
ji'kewa da ruwan hawaye,'kiyayyar abbu ta 'kara ninkuwa a
zuciyarta,domin tasan za'a rina,'kiyayyar abbu ga bilal ba'a banza ba!
Bilal ya dubi abbu cike da 'karfin hali yace 'wacce irin 'kiyayya ce
wannan? ,wani irin kishi ne wannan ? ,mahaifina ya baro 'kasar
haihuwarsa sanadiyar asirin da kayi masa,hakan yasa ya taho nigeria,kuma
ya kafa kasuwanci a garin kano,ya kuma auri mahaifiyata,haihuwa ta da
wata biyu ,ya tafi kasar haihuwarsa da niyyar zai je ya dawo ya tafi
damu,tafiyar da bai dawo ba kenan ba,sai mutuwarsa ce ta riski kunnuwar
mahaifiyata wacce itama ta rasu ina mai watanni goma uku a duniya' bilal
kuka ne ya subce masa mai zafi,yana mai cigaba da cewa'akan kud'i,akan
dukiya? ,ka aikata haka abbu,a lokacin daka gano cewa ni d'a ne ga d'an
uwanka maimakon ka jani a jiki,ka nunamin dangina da 'yan uwana ,sai ma
ka 'kara tarwatsa min rayuwata,ka nuna 'kiyayya ga yar cikinka don tace
tana so na da aure' ya goge hawayensa yace 'amma bakomai abbu
,ALHAMDULILLAH haka Allah ya tsara min rayuwata ,kuma a kullum ina 'kara
yin godiya gareshi,ka ci arzikin hibbatu,kuma ko da bazaka nemi
gafarata ba,ni na yafe maka,domin shirkar da ka aikata ma ya isheka'
,abbu kuwa ko a jikinsa ,domin kalaman bilal bai ratsashi ba ko
kad'an,duban bilal d'in yayi yace 'kaga! ni ban nemi jin wani dogon
surutu ba,ka sakar mini 'ya ' ,'ba zai saka ba!' hibbatu ta amsa tana
mai goge hawayen idanunta,abbu ya dubeta yace 'me kika ce?' ,'ba zai
sakeni ba ,kuma babu wacca zai saka a cikin mu,wallahi abbu ko da imad
ya auri ameera ,daga baya bilal yazo yace yana sonta toh wallahi sai na
kashe aurensu ,na aurawa bilal ameera,domin bilal a yanzu ya cancanci ya
samu duk wani farin cikin da ya rasa a baya,tun haihuwarsa bai samu
farinciki ba,yan uwan mamansa sun nuna mai 'kiyayya shi da kakarsa bayan
rasuwar mahaifiyasa,ya sha wahalar rayuwa ,kuma yazo ya aureni bai
tsira ba,sai ma karin wani bakin cikin wanda kaine sila,had'uwarsa da
alhaji da kuma aurensa da ameera ne yasa ya tsinci kansa a matsayin
dayake ciki a yanzu,bazai zamto ta sanadiyata bilal ya zama butulu ga
zuri'ar alhaji ba,bazan goyi bayan bilal ya saka alkhairi da sharri
ba,wajen sakar masu 'ya ba' hibbatu ta 'karasa kusa da bilal da meera,ta
ri'ke hannun bilal tana cewa 'no matter what,ina tare da mijina a
kowanne hali,kamar yadda nayi alkawari a baya ,ina tare da mijina a ko
da yaushe,kuma farin cikinsa shine nawa 'abbu a rikice ya kai duba ga
bilal wanda matansa suke tsaye a bayansa,yace 'oh khamis ya mutu,amma
duk da haka ya bar mugun iri a raye ' ,alhaji murya a kasaushe
yace'mugun iri ya wuce kai,mai ba'kin hali da mugunta,kwad'ayi gami da
kishi,shi yasa Allah ya jarabce ka da wasu irin 'ya'ya,ba banza ba
hibbatu ta zamo kwad'ayayyiya ,imad ya zamo mara yarda da kaddara,kuma
Allah ya sakawa khamis ta hanyar cusawa hibbatu soyayyar bilal,wanda
hakan yasa ta zamo mata a gareshi ,wato dai what goes round comes
arround! kayi gaggawar tuba ga Allah ,saboda ka tabka babban kuskure a
rayuwa' ,ammi idanunta na zubar da hawaye tace 'abbun hibbatu ka
cuceni,kuma ka cuci 'yay'ana ,da suka yo gadon halinka,dan ma Allah yayi
addu'ar uwa tana tasiri akan 'yayanta,hakan yasa abun nasu yazo a
saukake,tir da halinka wallahi,' abbu ya dubesu yace 'nifa ban bada
labarin nan ba,don kuyi min surutu ba,na bada labarinnan ne saboda a
sakar mini 'ya ,jini ne dai bazan had'a da khamis ba,tunda zafin talauci
bai korota ba,yanxu sai ta fito dan dole' ,hibbatu tayi caraf tace
'wallahi babu inda zan fito in je,domin labarin nan daka bayar shine ya
'kara min 'kaimin zama a gidan mijina,aure mutu ka raba' ta dubi bilal
da meera tana cewa'ku wuce mu tafi gidan mu',shigowar yan sanda ne yasa
kowa yayi turus yana dubansu in an d'auke imad...
Yan sanda suka 'karaso suna masu zare jajayen idanunsu,imad ne ya
'karaso garesu ,ya nuna bilal yana cewa 'arrest him' ,hibbatu a
mamakance tace 'arrest who?',imad ya bata da amsa da cewa 'barawon
mijinki mana' ,'satar me yayi maka?' meera ta jefi imad da tambaya ,imad
ya dubeta ya bata amsa da cewa'tambayata kike ,mayaudariya kawai,kin
san nace miki i'll never give up ,domin bazan ta6a bari wannan banzan ya
zama mijinki ba' TAS! hibbatu ta zabgawa imad mari tare da nunashi da
yatsa tace 'kar ka kuskura ka 'kara zagar min miji,domin mijina yafi
karfin wulakanci wllh' ,imad dafe da kumatu yace 'an ce masa banza
d'in,shi wanene in ba banza ba' tuni meera ta cire takalminta ta bugawa
imad a baki tana cewa 'banza ya wuce kai,mara zuciya kawai,bana sonka
ana dolene,mijina nakeso,kuma ka 'kara zaginsa,sai nayi maka fiya da
haka',imad dafe da bakinsa ya dubi yan sandan rai a 6ace yace 'what are u
waiting for? Arrest him?',alhaji ne ya dubesu yace 'ku dakata ko ma
menene ku bari kuji ta bakin mu' ,hajiya tace 'laifin me bilal yayi da
zasu bari su ji ta bakin mu' ,ammi ranta a 6ace ta dubi imad tace 'imad
meye haka,me bilal yayi maka da za ka sa yan sanda su tafi
dashi','fashin matata yayi mini,kuma wallahi sai an bimin hakkina'
hibbatu da gudu ta fad'a cikin gida,ta nufi kitchen ,ta sungumo katuwar frying pan mai d'an nauyi...
Musu ne ya kaure tsakanin su meera,hajiya,alhaji,ammi da kuma imad da
abbu ,su imad da abbu suna cewa a tafi bilal,su meera da ammi suna cewa
babu inda za'a tafi da bilal ,yan sandan kokarin gar'kamawa bilal ankwa
suke wanda shi tuni yayi mutuwar tsaye,hibbatu ce ta 'karaso hannunta
ri'ke da frying pan, ta dubi yansandan tace 'duk wanda ya kuskura ya
ta6a min miji a cikinku wallahi sai na mo'ka masa tukunyar nan' ,d'aya
daga cikin yansandan yace 'mu zaki kwad'awa tukunya,muna yan sandan'
meera tace 'yo in ma hitler ne ina ruwan mu,ku ta6a mana miji ku gani'
,ta nufi gate ita ma ta sungumo benci, ta dawo tana huci ,imad ne ya
dubi hibbatu yace 'wai ke ba HAYAR MIJINKI kika bayar ba ,ki
bari......!' hibbatu ce katseshi ta hanyar cewa 'in ma SADAKAR MIJINA na
bayar ina ruwanka,wallahi zan ran'kwala maka tukunyar nan idan baka ce
su fita daga gidannan ba',abbu yace 'babu inda zasuje,sai sun tafi da
wannan d'an iskan yaron,sai wani ji dashi kuke,wai ku masu miji' ,ammi
tayi caraf tace 'iskancin me yayi maka,da ke kiransa d'an iska' ,abbu ya
bud'e baki da niyyar bata amsa,amma ya kasa sanadiyar wani azababben
ciwon ciki da ya turni'keshi,hakan yasa ya dafe cikinsa,idanunsa sukayi
ja,tuni ya sulale 'kasa a sume.....
Hankali a tashe ammi ta kamo abbu tana jijjigashi,bilal ne ya 'karaso ya
d'aukeshi ,yayi waje dashi,imad tuni ya 'kirgo kud'i ya bawa yansandan
ya sallamesu ,tare da bin bayan bilal,dogarawa da suka gaji da jiransu
ammi ne suka bud'ewa bilal mota ganinsa cicci6e da abbu ,ammi ta shiga
motar itama tare da bawa dogarawan umarnin su wuce asibiti,alhaji ne ya
bawa maigadi umarnin ya bud'e gate,alhaji ya fito da katuwar mota ,suka
shige motar gaba d'ayan su,suka bi bayan su bilal,bayan sun yiwa ammi
waya ta fad'a masu sunan asibitin da suka nufa...
Emergency aka wuce da abbu ranga ranga,bai ma san inda kansa yake
ba,hakan ya bawa kowa damar yin sallar la'asar ,alhaji dasu bilal suka
wuce masjid d'in asibitin,ammi ,hajiya hibbatu da meera female masjid
suka shiga don gabatar da tasu sallar.
5:30pm likita ya fito daga emergency ,gaba d'ayansu suka nufeshi
musamman bilal da duk ya bi ya tada hankalinsa,suna tambayarsa ya jikin
abbu ,likita ya dubesu ya ce 'jiki da sauki ,an wuce da patient d'in
ammunity' ,bilal ne yace 'doctor me ya same shi' ,jim likitan yayi yace
masu su biyoshi ofis,duuu! Suka bi bayan likitan!
Bayan likita ya zauna ya dubesu one by one,su ma duk sun tsura masa
idanu,suna jiran abinda zai fad'a ,likita ya sauke ajiyar zuci yace '
kodarsa ce ta samu matsala duka biyun,wanda shi kansa bai san da
wanzuwar hakan a tattare da shi ba,sai da kod'ar nasa ya kai matakin
'karshe na lalacewa a yau d'innan,hakan ya janyo d'aukewar numfashinsa'
,imad cikin rud'ani yace'doctor u mean my father has a kidney failure?'
,'ofcourse yes,and all the 2 kidneys has failed ,if care is not taken
,he may loose his life in not less than 3days' ,'innalillahi wa inna
illaihi raji'un ' kalmar da kowa ke maimaitawa kenan!
[oh ikon Allah kenan,mutumin da yake ta surfa masifa d'azunnan cikin
koshin lafia,shine yanzu yake shirin she'kewa [oh ikon Allah
kenan,mutumin da yake ta surfa masifa d'azunnan cikin koshin lafia,shine
yanzu yake shirin she'kewa lahira]
Bilal ne ya dubi likita hankalinsa a tashe ,yace 'doctor ba yadda za'a
iya yi ne a ceto shi' ,likita yace 'toh! Mafita d'aya ce,kidney
transplant,kuma a yanzu we are out of it,and he has 3days left',alhaji
yayi caraf yace 'likita ko nawa ne zamu biya ,a samo 'koda a dasa masa
ita pls,do something about it' ,likita ya dubi alhaji yace 'abune mai
wuya ,domin kamata yayi a yi masa aikin gobe,kuma samo 'koda b4 2mrrw
zai yi wuya,sai dai in wani a cikinku zai yadda a cire nashi gud'a daya a
dasa masa' ,dif! Kake ji a d'akin babu wanda ya 'kara yin ko da
kwakkwaran motsine ballantana kuma magana,alhaji ne yayi 'karfin hali ya
nuna imad yace 'ga d'ansa nan,a cire tasa a dasa masa' ,imad a firgice
yace 'wa? Ni?,gaskiya i can't' ,hibbatu ce cikin shisshi'kar kuka tace
'ALLAH YA JIKANKA ABBU ' ,kowa ya amsa da 'amin' ,in ka d'auke bilal da
likita da suke zare idanu suna kallon kowa da mamaki,wato dai baza su
bada kodar su ba,bilal ne ya dubi likita yace 'doctor ni a cire tawa
guda d'aya a dasa masa' ,mamaki ne ya ziyarci kowa dake gun,musamman
hibbatu da ta 'karaso gun bilal tana kuka tana cewa 'kasan me kake fad'a
kuwa bilal,u r putting ur life at risk,ka kyaleshi ya mutu wa'adinsa ne
ya cika..' ,bilal ya katseta a kasaushe yace 'ke kina tabbacin zaki kai
daren yau a raye ' 'a'a!' ta bashi amsa ,'toh ki kyaleni,zan bada 'koda
ta a dasawa abbu ,ko da kuwa hakan na nufin zan rasa rayuwata' bilal ya
fad'a yana mai mi'kewa tsaye ,ya dubi likita yace'i'm ready doctor,the
transplant should carry on please!'
Hakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IHakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL