Ammi ce ta d'inga bubbuga bayanta ta sigar rarrashi tana cewa 'nutsu
hibbatullah ,ki gaya min me ke faruwa,domin nima nayi mamaki a lokacin
da naji zancen auren mijinki da ameera,hakan yasa ko da muka zo ,ban
biyo abbunku nashigo ba,domin ban san me zan tarar ba,ganin sun d'ad'e
ne yasa na biyo sahu,gaya mini meke faruwa ne,duk da imad yace wai
ameera ta auri mijinki a matsayin MIJIN HAYA ne',hibbatu ta shanye
kukanta ta labartawa ammi komai daga A har Z,sannan ta d'ora da cewa
'yanzu tunda imad d'in yazo i sai ya saketa ko?' ,ammi ture hibbatu tayi
daga jikinta ,ta dubeta duba mai d'auke da tir da halinki, a kausashe
tace'amma ke shasha ce hibbatu,yaushe kika zama haka,ina soyayyar da
kike ikirarin kina yiwa bilal ,ko da imad ya ce wai ameera MIJIN HAYA
zata aura ,naga sakarcinsa da wawancinsa,ashe kece ma kikayi kane kane
wajen bada Mijinki haya,ke a ganinki kinyi hakan ne saboda soyayya
ko,kinyi hakan ne saboda ki ceto ku ke da mijinki daga kangin talauci
ko,kin aikata haka saboda imad ya auri ameera ko?,amma kin manta da cewa
muna namu Allah na nashi,a yanzu babu wanda zaiyi la'akari da hakan
,domin ba'ayiwa namiji wannan tijarar,wato ke gaki uwarsa ko,wallahi ko
uwarsa ba tada wannan ikon akansa domin ba ita ta sassaka shi ba da har
zata d'aukeshi ta bada hayarsa' ,hajiya tayi caraf tace' gaya mata dai,i
namiji ko nakasasshe ne ,sai haka ,domin duk tsiya he's more superior
than her,dole ta bishi bawai ita ya bita ba,domin ba'a yiwa namiji
iko,muma nan data ganmu mazajen mu ke iko damu,so duk abinda ya faru ita
tajawa kanta ,domin babu wanda ya ro'keta da ta bada mijinta haya '
,hibbatu ta d'ora hannu aka tana rusa kuka tana cewa 'ammi ki taimakeni
ki sashi ya saketa wallahi na janye,nafasa bada HAYARSA' ,alhaji ya
amshe da cewa 'daman babu wanda ya amshi mijinki haya,aure mai sunan
aure aka d'aura tsakaninshi da ameera,domin bilal bai boye min komai ba,
dana tuntu6eshi da zancen aurennan,yanzu faruwar wannan al'amari zai sa
ku gane kurenku ke da kaninki, har da ita kanta ameerar' ,hajiya ta
d'ora da cewa 'balle kuma ita ameeran tana son mijinta ,bata d'aukeshi a
matsayin MIJIN HAYA ba' ,mutanen da ke gun sai kus kus suke suna
zund'en hibbatu ,hibbatu ta cigaba da zunduma kuka tana cewa 'wallahi na
janye,ciniki ya tashi,na fasa bada hayar,zan maido maku da
kud'inku,amma a barni da mijina ba tare da nayi sharing da wata ba'
,wata mata ce a cikin matan biki tace 'sannu mai miji,daman kin san kina
son mijin kika bada hayarsa' ,wata ta cafke tace 'kyale yar rainin wayo
mana ,d'azu da akayi shelar an daura auren nan, karkace hanci tayi tana
zuba gud'a , sai yanzu da taga idi zigidir ,zatace a warware auren' ,'i
wallahi bata isa ,zaman ameera a gidan bilal daram,ya zama dole mu
mi'kata d'akin mijinta wanda muke fatan mutuwa ce kad'ai zata rabasu'
cewar wata matar ,wata dattijuwa ta kama baki tace 'oh ni zaidabu
abu,ban ta6a jin inda aka bada miji haya ba ,sai akan wannan matar,kuma
inaga daga kanta ,baza a kuma samun macen da zata bada MIJINTA HAYA
BA!....
Haka matan suka cigaba da tofa albarkacin bakunansu,liman ne ya katse su
ta hanyar cewa 'toh ko ma dai menene,aurene an riga an daura' ya dubi
hibbatu yana cewa'dan haka yarinya sai kiyi ha'kuri,saboda yanxu za6i ya
ragewa shi mijin naki',a cikin mazan ne wani ya d'aga murya yace 'za6i
shine kar ya saki amaryarsa,an gaya mata cewa ana juya miji ne,kuma ana
sa shi yin abinda bai yi niyya ba,in har ya cika gwarzon namiji toh kar
ya kuskura ya biyewa matarsa ya saki amaryarsa',alhaji salis ne yace
'toh ya isa haka,biki da daurin aure an gama kowa yana iya
tafiya,mungode Allah ya saka da alkhairi' ,sum sum mutane suka fara
kad'a 'keyarsu suna tafiya,kowa da irin nashi ra'ayin akan lamarin
hibbatu data bada MIJINTA, HAYA!....
Hibbatu ta cigaba da rusa kuka tana cewa 'dan Allah kuce ya saketa,ku ce
mata ta 'kyale min miji ,na fasa bada hayar wallahi zan maida masu
kud'insu' ,alhaji ne ya katseta ta hanyar cewa 'babu zancen maido kud'i
,domin kud'i na d'an uwanki ne ,bana ameera ba' ,hajiya ta amshe da
cewa'har da kud'in baban nata,domin miliyan biyun da ya bawa ameera
kyauta,ita ameera ta bawa,kinga kenan ,sisin ameera baki ci ba,ya rage
naku dake da kaninki',hibbatu hannu ta d'aura akan kirji ,idanunta na
zubar hawaye ta dubi bilal cikin ido tana cewa 'yanzu sakayyar da zaka
mini kenan ,lallai namiji famfo ne ,bashi da tabbas,a lokacin da ka
zubar da ruwa da niyyar ka tarar wani,a lokacin ruwan famfon ke d'aukewa
d'if ba tare da notice ba,duk halaccin so dana maka a rayuwa bilal,da
abinda zaka sakamin kenan',bilal dubanta yayi a tsanake yace 'hibbatu!
halaccin da kika min a rayuwa ,saboda Allah kikayi min?,ko kuma saboda
ki d'inga juyani kamar masa akan tanda kika min halaccin? ,hibbatu kasa
bada amsa tayi,sai kukanta ma daya tsananta, hakan yasa bilal ya cigaba
da cewa 'ina zaman zamana,kika sani a gaba wai in auri ameera,kin bada
ni haya,kuma kin amshi kud'in hayar wato ni gani haja ko?,ni ko da
alhaji ya tuntu6eni da zance,gskiya na fad'a masa,kuma na sanar dashi
wasiyyar kaka a gareni,hakan yasa alhaji ya nemi da yayi maganar da
ke,ko hakan zai sa ki janye,amma da alhaji yayi maki zancen ,da kanki
kika amince gani kike kamar irin haka bazai ta6a faruwa ba,wato ke gaki
mai basira ko?,hibbatu ko a gun Allah banida laifi domin aurena da
ameera ba haramun bane' ,ammi ta amsa da cewa 'kwarai dagaske' sannan
tace' kaga kai ka tsaya yi mata dogon bayanin nan,d'auki matarka kawai
ku tafi,idan taga dama ta biyo ku,idan kuma wannan karatun bai isheta
d'aukan darasi ba,toh ita tasani',abbu cikin d'aga murya ya dubi bilal
yace 'tunda bazaka saki ameera ba,iyayenta sun d'aure maka gindi kar ka
sakar masu 'ya,toh ni ina son ka rubuta min takardar sakin hibbatu yanzu
nan,domin idan su sun ga dacewarka da zama mijin ameera,toh ni tun fil
azal banga dacewarka da zama mijin hibba ba,you don't deserve her as a
wife,ina son ka sakar min 'ya!'.....
A mamakance bilal ya maimaita kalmar 'takardar saki?' ,'eh takardar
saki' ,hibbatu ta maimaita a kausashe idanu jajir,ta cigaba da cewa 'ya
zama dole ka bani takardar saki na,domin ban shirya rayuwa da kai , tare
da wata a matsayin matarka,bilal in har bazaka saki ameera ba,toh nima
bazan zauna da kai a matsayin matarka ba',ammi ce cikin zafin nama ta
d'aga hannunta ta kwashe fuskar hibbatu da wani bahagon mari,wanda hakan
yasa hibbatu ta dafe kumatun nata da hannu biyu ,tana mai kallon ammi a
gigice,ammi ta nuna hibbatu da yatsa tana cewa 'ki dawo hayyacinki
kisan me kikeyi kuwa,ke har kin isa ki bud'e bakinki kice bilal ya baki
takardar sakinki,ina kika kai soyayyarsa da kike ikrarin kina masa,ya
kamata ki farka idan bacci kikeyi,domin rabuwarki da mijinki wallahi
shine mafi munin kuskuren da zaki tafka a rayuwarki,domin idan wauta da
sakarci sunyi miki jagora wajen bada mijinki haya,toh kar ki bari
fushi,kishi da kuma dokin zuciya suyi miki jagora wajen tafka wani
babban wautar,wato amsar takardar saki a gun mijinki,kar ki sake ki
biyewa abbunki,domin abbunki kansa kawai ya sani'
Bilal matsowa yayi kusa da hibbatu ya ri'ke hannunta yana shafa
kumatunta yace 'kisa ranki a inuwa hibbatu,ni da ke mutu ka raba,ko
menene zai faru ,baki na bazai ta6a furta miki saki ba,yatsuna baza su
ta6a rubuta miki saki ba' ,a zafafe hibbatu ta kwace hannunta ,cike da
karaji tace 'in har soyayyar da kake mini babu algus a cikinta ,ina son
ka saki ameera ka bata takardarta,free her 4rm the clutches of this
arranged marriage ,i want u 2 free her!',bilal shiru yayi kawai yana mai
zuba mata idanu.
Imad wayarsa ya ciro, ya ja gefe ,ya buga waya ,murya 'kasa 'kasa ya
bada adireshin gidansu meera yana mai cewa a turo masa yansanda
gidan,'it's urgent cause it's a robbery case',yana gama wayar yayi
murmushin mugunta a zuciyarsa yana cewa 'bilal yau da kai da matarka,sai
kun kwana a cell,zaku gane cewa ,kokarin rabani da meera da kuke shirin
yi,shine ganganci mafi kasada da kuke shirin aikatawa'..
Abbu kamar wani zautace ya dam'ki bilal yana cewa'na tsaneka,na tsaneka
bilal,tsanar danake wa khamis,ita ta shafeka' bilal a mamakance ya dubi
idanun abbu yana cewa 'meye had'inka da mahaifina,wacce ala'ka ce
tsakaninku?' ,'ala'ka ta jini,ubanmu d'aya,uwa kuwa kowa da tasa' abbu
ya bashi amsa ,sannan ya cigaba da cewa 'ina son ka bud'e kunnuwanka da
kyau , ka ji wannan ta'kaitaccen labarin da zan baka,domin ina fatan
hakan ya zamto sanadiyar da zaka sakar min 'ya!'.......
Bilal,hibbatu,meera,imad,ammi,hajiya da alhaji!
Mamaki ne ya bayyana akan fuskokinsu karara, dalilin furucin abbu!
Abbu ya cigaba da magana kamar haka:
mahaifiyar khamis ta kasance ita ce mace ta farko da mahaifina ya
aura,bayan shekara biyu da aurensu,aka bawa mahaifina sarauta hakan yasa
ya 'kara aure ,wato ya auri mahaifiyata,bayan wata goma da aurensu
,mahaifiyar khamis ta haifi khamis,khamis na da shekara biyu aka
haifeni!
Daga haihuwata ba'a kuma haifan wani d'a namiji ,sai 'ya'ya mata
kawai,sai ya kasance ni da khamis ne kad'ai y'ay'a maza,khamis ya
kasance mai 'kokari da hazaka a komai da ya sa gaba a rayuwa,a boko yayi
min fintinkau a islamiyya ma haka,sai ya kasance kowa a fada naji
dashi,kowa yabonsa yake,haka zalika tawa mahaifiyar da yan uwana,domin
ko fad'a zata min sai tayi min misali da khamis,hakan ya haifar mini da
tsanarshi matu'ka a zuciyata,domin ya kasance centre of attraction 2
everyone!
Lokacin da nake final year a university ,a lokacin khamis ya kamalla
masterx d'insa,a wani hutu ne dana zo,kwatsam sai na samu labari wai
mahaifina zai yi marabus ya nad'a khamis a madadinsa,kuma gaba d'aya
dukiyarsa zai koma hannun khamis ya cigaba da juyawa,ni ban damu da
sauratar ba,amma batun dukiyar ne ya tsaya min a rai,hakan yasa naje na
samu mahaifiyata ina fad'a mata gsky ba'a min adalci ba,fad'a da nasiha
tayi min sosai !
Mahaifina da kansa ya kirani yake sanar dani cewa dazarar na kamalla
karatuna,i'll be joining khamis in the family business as an assistant 2
him,wannan hukuncin bai min dad'i ba ko kad'an ,hakan yasa na d'au
mataki naje gun wani baban malami a 'kasar tamu,masanin taurari,na nemi
da ayiwa khamis [tunkud'e]!
Bayan sati d'aya kwatsam khamis ya had'a ina shi ina shi ya bar gidan ba
tare da yayiwa kowa sallama ba,naji dad'in faruwar hakan a
zuciyata,amma a fuska na fi kowa nuna damuwa,anyi cigiya amma ba
labari,har kasashen larabawa dake kusa da 'kasar tamu duk an tura ,amma
duk amsa d'aya ce 'he's no where 2 be found' ,sanadiyar haka mahaifinmu
ya kwanta ciwo ,har ciwon yayi ajalinsa,an so a bani sarautar,amma nace
bana so ,hakan yasa sarauta ta bar gidanmu ta koma hannun 'kanin
mahaifinmu da zuri'arsa,ni kuwa na had'a kan dukiyar mahaifinmu gaba
d'aya na cigaba da juyawa,ina business,ina tafiye tafiye daga 'kasashen
larabawa har zuwa africa[ku koma asalin hibbatu]!
Na manta da khamis da batunsa a rayuwata ,kwatsam sai ranar dana ganka a
guest parlour tare da hibbatu,ina ganin fuskar ka ,nasan cewa 'u look
exactly like my brother but i'm not sure,sai da hibbatu ta sanar dani
tarihinka,na gasgata hasashena a kanka,dalilin da yasa na 'ki amincewa
aurenka da hibbatu kenan,ganin ta nace ne yasa na hakura nayi mata auran
wulakanci,kuma na cigaba bibiyar rayuwarku,duk inda kukaje neman aiki
,ni nake hanawa a baku aikin,nayi hakan ne,saboda idan hibbatu ta gaji
da rayuwar talauci ,nasan zata dawo garemu,duk halin da kuke ciki ina
sane,kuma ni na hana ammi da danginta su taimaki hibbatu,a lokacin daka
samu aikin gadi a gidannan ,ba yadda na iya ,domin nasan inna ce alhaji
ya koreka,xai nemi yaji dalili,kuma ni na riga nace masu hibbatu ta
rasu,ko a ranar da muka zo, ka bud'e mana gate na ganeka,ita ma hibba na
ganeta a lokacin da ta kawo mana cups duk da ta shafa wani abu a
fuskarta' ,abbu ya dubi bilal yace 'ni ne silar kasancewarka cikin
talauci tun daga ranar da hibbatu ta zama mata a gareka,zaka cigaba da
zama da matar da mahaifinta yayi maka mugun illa a rayuwarka?'....
Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee isma'il