Hibbatu tayi parking motarta a parkn space,ta fito daga motar,ta 6ude
booth ta fito masu da kayansu,bilal ya rufo gate d'in tare da isowa ga
hibbatu ya taya ta kwasar kayan suka shiga ciki ,d'aki mai d'auke da
mini parlor & toilet hajiya ta kaisu ,sannan tace masu in sun kimtsa
su fito su karya ga abincinsu akan dining,hibbatu zuciyarta fari sol
kamar kankara don murna,domin ita kanta tasan ta dawo cikin arzikin da
tayi hannun riga dashi shekaru 6 da suka wuce...
Bayan sun kimtsa suka fito,dinning suka nufa suka karya kumallo,hibbatu
ta kwashe kwanuka ta kai kitchen ,bilal kuma alhaji yace ya d'auko
takardunsa su tafi....
Ko da suka fito alhaji yaga motar hibbatu bai yi mamaki ba domin yasan
kwanan zancen,direba ne ya fito da mota ,alhaji da bilal suka shige,ya
jasu suka fice...
* * *
Alhaji ya yaba da takardun bilal bayan ya duba,hakan yasa ya nad'a bilal
a matsayin assistant managing director na kamfanin [goni motors],kuma
ya bawa bilal damar ya za6i mota guda a cikin motocin kamfanin,bilal sai
hawaye yake yana yiwa alhaji godiya,bai tsinke da lamarin alhaji ba sai
da suka wuce boutique/mall ya siya masa tufafi ,casual nd office
outfit,dangin turare,takalma,agogo,ready made native outfits,huluna da
cufflinks,laptop da waya,sannan suka garzaya men salon,akayiwa bilal
aski ,tare da wankin kaushin kafa,aka kuma yanke masa farata,sannan suka
fito suka wuce gida da zummar gobe bilal zai fara zuwa ofis ,kuma after
office hours za'a dinga koya masa motarsa har ya iya....
*BAYAN SATI DAYA*
shirye shirye ya kankama,hajiya ta tisa hibbatu da meera a gaba suna
zuwa yawon gyaran jiki da siyayyar kayan fitar biki da sauransu,domin
alhaji ya sakarwa hajiya kud'i,ita kuma bata nuna banbanci tsakanin
hibbatu da meera,domin tare dasu take ficewa,su za6i abunda ransu ke so
,ita kuma aikintashirye shirye ya kankama,hajiya ta tisa hibbatu da
meera a gaba suna zuwa yawon gyaran jiki da siyayyar kayan fitar biki da
sauransu,domin alhaji ya sakarwa hajiya kud'i,ita kuma bata nuna
banbanci tsakanin hibbatu da meera,domin tare dasu take ficewa,su za6i
abunda ransu ke so ,ita kuma aikinta biya!
Gidan gadon bilal kuwa aiki yayi nisa,domin har an d'aura dekin anata aiki ba kama hannun yaro...!
Bilal yayi kyau yayi fresh,balarabe sak,kana ganinshi kaga jinsin
larabawa haka zalika hibbatu,yana zuwa ofis kuma ana koya masa mota in
ya tashi ofis!
sabon maigadi aka kawo gidan,kuma mai aikin hajiya ta dawo itama,kowa a
gidan ya shiga busy ana ta shirye shiryen biki ,musamman alhaji da ya
tafi dubai domin had'owa meera lefe ,ita kuma hibbatu kayan fad'ar
kishiya,da kuma kayan d'akinsu....!
Hakkin mallaka
Ana sauran kwana uku alhaji ya dawo daga dubai da kaya niki
niki,akwatuna 6 akayi kowaccensu komai iri d'aya kuma ba banbanci sai na
kala,haka zalika kayan d'aki irinsu furnitures da household equipments
duk alhaji ya siyowa meera da hibbatu!
Masu gyaran gidan gadon bilal tuni sunyi nisa fenti kawai ya rage,aje ayi jere!
Amarya meera da kishiyarta hibbatu ,sunyi kyau har sun gaji,domin gyara kam sun sha shi.
Bilal kuwa aiki yasa a gaba tukuru,baya wasa da zuwa ofis,kuma motarsa
tuni ya fara tu'kawa da kansa,amma duk da haka an makala mai tambarin
harafin 'L' a gaba da bayan motar...
Hibbatu duniya sabuwa,banza ta samu,ina aljannah ta jefa hajiya da
alhaji,a kullum sai taci kaza da tsiren hanta da madara confirm!
Bilal da ameera kuwa ,ba sa had'uwa sai a gun cin abinci,kuma ko da sun
had'u gaisuwa da d'auke kai ke shiga tsakaninsu ,alhaji shi bai damu
ba,domin yasan dawar garin,ita kuma hajiya ta d'au haka a matsayin kunya
da kawaici!
*CYPRUS*
Abbu hakimce akan kujera yana shan kankanar da ammi ke yanka mai tana
mi'ka masa,wayarsa tayi ringing,ammi ta mi'ka masa,ya d'auka tare da
karawa akan kunnensa,muryar alhaji ce ta masa sallama ,abbu ya amsa yana
cewa 'my friend ya kake,ya kowa da kowa' 'lafiya lau,ya imad da
amminshi' 'suna nan lfy' abbu ya amsa ,alhaji ya cigaba da cewa 'my
friend daman na bugo ne in sanar da kai cewa gobe d'aurin auren
ameera,nasan bazaku samu chance d'in zuwa ba,amma addu'arku muke nema'
,abbu ya washe baki yana cewa 'toh toh masha Allahu abu yazo,ALLAH ya
sanya alkhairi,wa zata aura kuma d'an gidan waye' 'd'an adam ne shi
kamar kowa,bilal sunansa ,kuma shine maigadin da ya bud'e maku gate da
kuka zo rannan,nasan ka ganeshi ko?' alhaji ya tambaya! A razane abbu ya
tashi da karfi ya maimaita 'BILAL? MAIGADI?' alhaji ya amsa da 'eh
bilal,amma maigadi a da,yanzu na nad'ashi assistance managing director
na kamfanin motocina' ,a zafafe abbu ya katse wayar bai jira sunyi
sallama ba,sannan yayi jifa da wayar yana huci ,ammi tayi sororo tana
kallonsa,hannunta ri'ke da wu'ka da kankana!
Abbu abin duniya ya isheshi sai maimaita sunan bilal yake,a daidai
lokacin imad ya shigo falon da sallama,abbu ne ya tareshi da tambaya
'kasan cewa gobe ne d'aurin auren ameera,dazu ubanta ya bugo yake
gayamini' ,imad da yake yasan MIJIN HAYA meera zata aura ,sai kawai yayi
murmushi yace 'ALLAH ya sanya alkhairi' 'ba amin ba!' abbu ya furta a
kausashe sannan yace 'kana nufin ka hakura da ameera kenan' 'eh abbu
,idan har haka zai faranta ranka' ,abbu idanu jajir yace 'toh ayanzu
babu abinda zai ba'kanta min rai face auren ameera da wani banza,kaje ka
sama mana ticket ,yau zamu wuce nigeria,da kai za'a d'aura wannan auren
gobe' ,imad cike da murna yace 'dagaske abbu ,daman fa meera MIJIN HAYA
zata aura' ,ammi da sai yanzu ta tsoma baki tace 'MIJIN HAYA ?' ,abbu
yace 'me kake nufi da kalmar MIJIN HAYA',imad nan take ya kwashe yadda
sukayi da meera ya gaya masu ,abbu ne ya dubeshi ranshi a 6ace yace
'amma imad kai wawa ne,gangariyar sakarai,kana wani batun MIJIN HAYA
,kasan wanene mijin da ameerar zata aura gobe ?' a sanyaye imad ya
girgiza kansa yana cewa 'bansani ba,kuma idan na kira wayar meera a
kashe nake jsamunta' abbu a da'kile yace'toh wanda ameera zata aura ,ba
kowa bane face bilal mijin 'yar uwarka,wanda na baka labarin cewa ta
za6e shi akan mu' ,imad zare idanuwa yayi yace 'mijin yaya hibbah ,meera
zata aura?' abbu ya amsa da 'ehmana idan ka tsaya sanya ,yanzu kaje ka
sama mana ticket,dole mu tafi nigeria a yau ,domin bazan bari a daura
auren bilal da ameera ba,idan bilal yayi nasara a baya wajen aure mini
'ya ,toh wallahi wannan karan bazaiyi nasarar auren matar da d'ana yake
so da aure ba....
Imad a fusace ya fice ya wuce airport,abbu ya kasa zaune ya kasa
tsaye,zuciyarsa sai tafarfasa take,yana nanata sunan bilal akai
akai,ammi kuwa ko a collar rigarta,domin tunda aka riga aka mata katanga
da 'yarta ,toh ita bataga abinda zai kuma d'aga mata hankali ba ga
lamarin abbu!
Imad kuwa a airport ticket bai samu ba,duk iya kokarinsa na ganin ya
samu ticket ,amma hakan ya ci tura ,saboda duk an riga anyi booking
flights d'in yau ,sai dai kuma na washegari,haka ya biya kud'i ya kar6o
tickets ,da zummar gobe sai subi morning flight..
Abbu ranshi bai so hakan ba,yaso yau dare yayi masu a nigeria,amma duk
da haka ya d'au alwashin sanya reza da almakashi ya warware auren meera
da bilal ko da kuwa ansa zaren 'karfe an d'inke masu auren....
*KANO NIGERIA*
Anata shirye_shirye,babu wani biki da za'ayi,daga d'aurin aure sai walima a kuma mi'ka amarya gidan aurenta!
Gida ya fara cika da yan uwa dangin hajiya da alhaji,gidansu hibbatu an
gyareshi tas,gida yayi kyau ,anje anyiwa amarya da uwargida jere bisa
jagorancin Gida ya fara cika da yan uwa dangin hajiya da alhaji,gidansu
hibbatu an gyareshi tas,gida yayi kyau ,anje anyiwa amarya da uwargida
jere bisa jagorancin hajiya!
hibbatu kuwa cewa tayi bazata koma gidanta ba saida amarya ameera,bilal kad'ai ne ya tattara ya koma gidan...
Kowa mamakin hibbatu yake yadda aka ga kishiya ta za'ke a bikin
kishiya,wasu na jin haushinta ,wasu kuwa burgesu take [basu san cewa
MIJIN nata ita da kanta tabada HAYARSA ba]
*RANAR DAURIN AURE*
Misalin karfe 1:00pm jirgin su abbu ya iso filin airport din kano,daga
fada aka turo masu motoci,domin ammi ta sanarwa kishiyar mahaifiyarta
zuwansu,ko da kuwa aka d'au hanya,abbu ya umarci dogarawa da su wuce
dasu gidan alh.salis goni!
A daidai wannan lokacin farfajiyar gidan alh.salis goni cike yake da
manyan mutane,dangi da yan uwa,cikin gida kuwa mata ne ke ta hidindiA
daidai wannan lokacin farfajiyar gidan alh.salis goni cike yake da
manyan mutane,dangi da yan uwa,cikin gida kuwa mata ne ke ta
hidindimu...
Amarya ameera da kishiyarta ansha kyau,sunsha kunshi,kaya iri d'aya suka sa,amma akwai banbancin kala...
Alhaji ne waliyyin bilal,limamin massallacin layin ya zamo waliyyi ga
ameera,bayan an zazzauna ,a take alhaji ya kirgo dubu hamsin ya
mi'ka,aka shafa fatiha ,kowa ya shaida d'aurin auren bilal da meera,a
take wani maro'ki ya karkace murya yana mai cewa 'AN DAURA AUREN BILAL
KHAMIS DA AMEERA SALISU BISA SADAKI DUBU HAMSIN .LAKADAN BA AJALAN BA'
,hakan kuwa yayi daidai da shigowar abbu da imad farfajiyar gidan!
Hibbatu dake tsakiyar mata a falo,jiyo abinda maro'ki ya fad'a ne yasa tuni ta ri'ke hanci ta fara zabga gud'a......
Tana gama yin gud'ar ,ta wuce d'akin meera a sukwane sai bin ta ake da
kallo,masu jin haushinta nayi hakazalika wanda ta burgesu sun yaba,a
zaune ta tadda meera ta zuba uban tagumi da hannu biyu ,hibbatu ta
'karasa ga meera,ta dafata tana cewa 'ameera nasan zakiyi ba'kin ciki da
wannan aure,domin gani kike kamar kin rabu da imad ko? ,toh kar ki damu
sam ,aurenki da bilal na nufin tabbatuwar aure tsakaninki da imad'
,meera bata tankata ba,amma zuciyarta cike take fal da farincikin
d'aurin aurenta da bilal ,a fuska ne kawai bata nuna ba....
Abbu gadan gadan ya nufi gurin da aka gudanar da daurin auren ,imad yana
biye dashi ,alhaji da hanzari ya tashi yana cewa 'barka da zuwa alhaji
shoaib ,ashe zaku samu damar hallatar d'aurin auren ameera ,ku zazzauna
,kuma gashi an riga an daura auren' dakatar da shi abbu yayi ta hanyar
cewa'ba zama ne ya kawo mu ba,kuma ba wai mun zo mu hallaci wannan
daurin auren bane,munzo ne domin a warware wannan aure kuma a daura da
imad',alhaji yayi caraf yace 'dalili?' cikin hargagi abbu yace 'saboda
ameera bata dace da wannan ba' yana mai nuna bilal da yatsa ,sannan yace
'da imad ta dace,kuma kai kanka kasan cewa imad da ameera suna matu'kar
son junansu' ,alhaji murmushi yayi yace'toh in banda abunka alhaji
,imad din ya shirya yin auren ne,ya kamalla ph.d din ne,is he matured
enough 2 get marry now?' ,abbu ransa a 'kuntacce yace 'duk abar wannan
maganar,ni dai kawai so nake a warware aurennan,a kuma d'aura da d'ana '
'baka isa ba !' alhaji ya bashi amsa yana cewa 'aure an riga an
d'aura,kuma kai baka isa ka datse ran auren ba,in har dai ba lokacin
cikawarsa ne yayi ba,ka manta lokacin da na d'inga binka da zancen auren
,amma fafur ka ki amincewa ,kace idan ta samu miji tayi aurenta ,amma
bilal sai ya gama ph.d yayi settling down xai yi aure,sai kuma kwatsam
don son zuciya ,yarinya an d'aura mata aure ayau ,sai kazo kana neman ka
tsige ran auren,toh wallahi baka isa ba' ,abbu cike da mamaki yace
'alhaji salis ni kake cewa ban isa ba ' 'eh baka isa ba ,naga 'ya tawa
ce kuma ni nake da iko da abata' cewan alhaji,mutane kuwa cirko cirko
sukayi suna kallon ikon Allah ,imad a fusace ya juya ya shige cikin
gidan ,d'akin meera ya wuce batare da ya dubi matan da suke zaune a
falon ba,yana shiga d'akin, murya a kasaushe yace 'meera waccan da aka
d'aura maku aure dashi ,shine MIJIN HAYAN?' ,'eh shine!' hibbatu tayi
caraf ta bada amsa tana washe baki ta cigaba da cewa 'mijinane na bata
hayarsa(nan ta kwashe yadda ta tsara lamarin ta labarta masa) ' ,tsaki
imad yaja yace 'toh fad'i ba'a tambayeki ba,ki kyaleni in yi magana da
wacce zanyi,domin tsakanina dake babu wata ala'ka' ,ya dubi meera wacce
batace kanzil ba yace'ina son ki fita yanzu ki amso takardar saki a
gunsa,domin aurenki zanyi ,HAYAR tayi expire tunda gashi na dawo'
,hibbatu da hanzari ta mi'ke tana cewa 'bara naje na amso mata takardar
sakin ,tunda mai abu yazo' tana shirin ficewa,meera ta daka mata tsawa
tana cewa 'kar ki kuskura kiyi wannan gangancin ,domin ban aike ki
ba,ban kuma baki umarnin yin hakan ba' ,hibbatu ta juyo tana zare idanu
,ta kalli gefe da gefenta ,sannan ta nuna kanta tace 'dani kike magana?'
,'eh da ke nake magana,ko sai na sake maimaita miki ne?' meera ta bata
amsa ,wani 'kara cikin hibbatu ya bada 'kulululululu....
Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee Hakkin Mallaka:abdulaziz ililee isma'il