Imad shima wanda mamaki ya gama samun matsuguni a zuciyarsa,sanadiyar
furucin meera ,dubanta yayi yace 'meera me kike nufi da kar ta kuskura
tayi miki wannan gangancin,ko kin fi so ki amso takardar da hannunki ne '
,meera ranta a 6ace tace 'ko kad'an ,kawai ban shirya amsar saki bane a
yau,it's a decision that i've 2 make on my own,bana bu'katar ku a yanzu
cikin wannan lamarin,u pple hv already played ur roles,it's time for me
2 play mine' ,hibbatu ta dubi meera tace 'ni fa bangane inda kalaminki
suka dosa ba,naga all u wanted is 2 marry imad,kuma lokaci yayi yanzu da
hakan zai faru,bilal bai riga ya d'ora maki idda ba,kuma we never
planned cewa zai d'ora miki idda,all this MIJIN HAYA stuffs was planned
only for the two of u 2 get married whenever abbu grant imad the
permission 2 get marry ,so what's act all for?' hibbatu ta tambaya ,
,meera tayi murmushi tace 'hibbatu waya kawo shawarar auren MIJIN HAYA?
'imad!' hibbatu ta bata amsa,
'na amince?' meera ta tambaya
'a'a!' hibbatu ta amsa
'waya tursasa ni in amince?'
'ni ce!'
meera tace 'na ro'ke'ki ki bani HAYAR MIJINmeera tace 'na ro'ke'ki ki bani HAYAR MIJINKI ?'
'a'a!' hibbatu ta amsa,
Imad ne ya katsesu ta hanyar duban meera yana cewa 'yanzu abin nufi a
nan shine bazaki fita ki amso takardar saki a gun MIJIN HAYA ba ko?'
'eh' meera ta bashi amsa 'sai yaushe ?' imad ya tambayeta 'sai ranar da
na daina numfashi' ,imad a firgice yace 'kina nufin cewa mutuwa ce
kad'ai zata rabaku da shi' ,'eh haka nake nufi' ,dariya imad yayi sosai
sannan yace 'ke kina da ya'kinin cewa shi zai amince ya zauna da ke har
abada,kuma bayan shi da kanshi yasan cewa MIJIN HAYA yake a
gareki',hibbatu wacca ita tafara gajiya da jin kalaman bakin meera sai
cewa tayi 'ya zama dole bilal ya sakeki ko da kuwa hakan na nufin cewa
bazaki auri imad ba ,kuma yanzu zan fita inje in amso maki takardarki,
ya rage naku da ku daidaita kanku' 'tabbas idan har kika bari hakan ya
kasance ,toh zan baki lada mai tsoka,tunda na lura ke akan kud'i babu
abinda bazaki iya ba' cewar imad ga hibbatu , 'ka ri'ke ladan da za ka
bani,domin ko da kud'i ko babu ya zama dole in sa bilal ya saki
ameera'...
Hibbatu ta juya da niyyar ficewa daga d'akin meera ta tsayar da ita ta
hanyar cewa 'ina son ki san cewa ko da ki amso min takardar saki a gun
MIJINA ,wallahi ban saku ba ,domin zan iya yin komai dan ganin na
mallaki burin raina ,wato MIJINA' 'mijinki?' ,hibbatu da imad suka had'a
baki wajen tambayarta 'eh mijina na kaina ba MIJIN HAYA ba,kamar yadda
kuke jifansa da wannan sunan! Meera ta cigaba da cewa 'hibbatu in bazaki
manta ba, na ta6a gaya miki cewa zan so in auri imad saboda kaucewa
wani bakon al'amari da ke shirin faruwa a gareni,wannan bakon al'amarin
ba komai bane face soyayyar MIJINA wato Bilal, dana kamu dashi a lokacin
da kika gama bani labarinki ,soyayyar imad na nemata na rasa a zuciyata
saboda kiyayyar danake wa abbu ne ya shafeshi,domin abbu shine silar
bakin cikinki,bakin cikin bilal,bakin cikina da imad a wannan
lokacin,nayi kokarin in ga na tsige soyayyar mijinki daga zuciyata
.saboda ina gudun zama mace mai cin amanar aminci ,wato amincin dake
tsakanina dake,imad bai gama fita a raina ba sai a lokacin da ya zo mani
da batun MIJIN HAYA,hakan yasa soyayyarsa ta fice mini a rai,na kuma
hakura dashi ko da kuwa zai kasance shine autan maza,kwatsam bayan na
gaya miki yadda mukayi da imad akan batun MIJIN HAYA,sai kikazo da wata
gurguwar shawara ko kuma in ce wauta wanda hakan yayi daidai da Mallakar
cikar burina,naso 'kin amincewa,amma kika tursasani da lallai sai na
amince na auri mijinki a matsayin MIJIN HAYA,na amince kuma nace miki da
kiyi kuka da kanki a duk lokacin da wani abu ya biyo baya,kuma bakomai
ne zai biyo baya ba illa ni ban d'auki mijinki a matsayin MIJIN HAYA
ba,kuma zan shiga gidansa a matsayin matarsa wacce nake fatan rabuwarmu
zai zamto ta silar d'aukewar numfashinmu wato mutuwa' hibbatu wacce ta
gama ji'kewa da gumi tace 'tirkashi,lallai meera kin cika makira ,mai
cin amana,daga taimako?' ,meera ta katseta tace 'babu wani
taimako,kwad'ayi,wauta,rashin tawakalli da yarda da kaddara ne ya jawo
maku duk halin da kuke ciki ke da kaninki a yanzu,uwa uba kuma ,rashin
jin maganar iyaye' ,imad da duk yagama fita daga hayyacinsa idanunsa ya
rine da kalar bakin ciki yace 'meera kina nufin cewa ,soyayyar MIJIN
HAYA ne yasa kika daina d'aukan wayata kuma inna kira in jinta a kashe'
'kwarai kuwa imad ,domin a ranar da sis hibbatu tazo ta sanar dani cewa
abba yasa ranar aurena da bilal,a ranar na karya sim d'in wayata nayi
flushing a toilet,domin na zama mallakin wani,wato mallakin bilal,kaga
kenan bani da wani ala'ka da kai, a yanzu maganar danake maka ma haramun
ne,domin kai ba muharramina bane,kuma ina son ka fice mani daga d'aki
right now,kuma ka d'auka cewa duk abinda ya faru ,yin Allah ne ,ba yin
mu ba' ,imad ranshi a 6ace yace 'meera bazan ta6a yarda ki su6ucemini
ba,domin i'll make sure i get married 2u ,because i'll never give up'
,dariya meera tayi tace 'i have the same disease but different name 'i
will never give in ,cause Allah is with me '.....
Hibbatu zuciyarta na tafasa tace'ameera idan ke kina son mijina,toh ina
da tabbacin cewa shi baya sonki ,domin ni tursasa masa ya aureki a
matsayin MIJIN HAYA a gareki,kuma haka zalika yanzu zan tursasa masa ya
sakeki domin HAYAR tayi expire',tana gama fad'in haka, ta sa kai ta fice
a fusace,imad shima ya fice dakin bayan ya cewa meera 'we shall see'...
Hajiya wacce tun shigowar imad d'akin ta biyo sahu,amma maganganu da
taji sunayi ne yasa tayi turus! ,sai da hibbatu da imad suka fito wanda
basu lura da tsayuwarta ba,sannan ita ma ta shiga d'akin ,meera tana
zaune d'a'bas akan gado ta dafe kanta da hannayenta ,wato kan nata ya
d'au chaji,hajiya ta 'karaso ta zauna kusa da ita tana cewa 'ameera ki
fito dani duhu,ki fahimtar dani ala'kar dake tsakanin hibbatu da imad
,ki kuma fayyace mini ma'anar kalmar MIJIN HAYA danaji kuna ambata
',tiryan tiryan meera ta labartawa hajiya komai tun daga ranar da taje
bikon hibbatu har izuwa yau ranar d'aurin aurenta da bilal,hajiya sai
gyad'a kai take tana jinjina lamarin ,tace 'tirkashi za'a yita kuwa
,hibbatu bata isa ba ,sai kace ita ce uwar da haifeshi,ta yi kad'an
wallahi,amma bazan d'au hukunci a yanzu ba, idan har hibbatu ta yi
nasarar amso miki saki gun bilal ,toh tabbas zata sha mamaki na,haba ni
fa ince,ina aka taba yin mace a wannan zamani da zata nuna za'kewa a
bikin kishiya,har ina tayata jin haushi abin,ashe ita ta d'au MIJIN ta
bada HAYARSA,sai kace ita ta sassa'kashi,ko ina aka ta6a yin haka oho
,wai ka d'au d'an adam ka bada HAYARSA,wani abin sai hibbatu',meera kuwa
bata 'kara tofawa ba,domin zuciyarta cike take taf da tausayin
hibbatu...
A farfajiya kuwa,abbune yayi ta surfa bala'i da masifa yana cewa ya zama
dole bilal ya saki meera,ko da kuwa meera baxata auri imad ba,har ta
kai abbu ya cakumi bilal yana cewa 'kasan Allah wallahi tallahi sai ka
saki ameera ,domin idan d'ana ya rasa ,toh kai baka cancanci ka samu ba'
,bilal yayi wani guntun murmushi yace 'abbu kenan ,wallahi ko 'yar daka
haifa kake da iko da ita ,baka isa kace in saketa ba ,kuma in saketa
ba,ballantana 'yar da baka da iko da ita' ,kalaman bilal sun konawa abbu
rai ,hakan yasa a harzuke yace 'kaga shegen yaro,ni kake cewa ban isa
ba,wai me kake takama dashi ne ,kai talaka ne, matsiyaci,uwa uba ga
rashin dangi da asalin uba',bilal yace 'a haka kuma na auri mata yayan
masu arziki,masu kuma dangi da asalin uba,kaga kuwa babu yadda Allah
baya tsara lamarinsa' ,sannan yasa hannu ya 6an6are hannun abbu daga
jikin rigarsa yana cewa 'ALLAH shine gatan bawa ,ba mutum ba ko kuma
dukiya'....
Hibbatu ta fisgi mayafi daga gun matan dake zaune a falo,ta kuma d'au
biro da takarda akan tv stand sannan ta wuce farfajiya,'karasawa tayi
gun ,ganin mutane sunyi cirko cirko,alhaji fuskarsa ta rine da ba'kin
cikin tozarcin da abbu yayi masa,abbu kuwa yana tsaye yana zazzaga
masifarsa kamar ya ari baki ,wai shi a dole bilal yayi masa rashin
kunya,hibbatu kuwa ganin haka bai sa ta fasa abinda ya kawo ta
ba,murmushi tayi ta dubi bilal tana mi'ka masa takarda da biro tace
'ungo ka ratattaba mata saki uku akan takardar nan,ciniki ya tashi,HAYA
yayi expire ,mai abu da kansa yaxo',imad ya cafke yace 'ga zahiri,nine
imad permanent mijin meera,not temporary' ,ta tagar da'kin meera hajiya
ta hango hibbatu tana mi'kawa bilal takarda da biro ,hakan yasa ta nemi
mayafi a d'akin ta yafa ,ta finciki hannun meera tana cewa taho
muje,ganin hajiya ta fice ri'ke da hannun meera yasa mata yan bikin suka
mara masu baya kowacce tana cewa Allah yasa lafiya!
Bilal batare da ya amshi takardar da biron ba ya dubi takardar da ita
kanta hibbatu,yana mai cewa a zuciyarsa 'hibbatu karfin hali,amma zaki
gane shayi ruwa ne' ,hibbatu ta katse mashi tunaninsa, tace 'bilal me
kake jira ne ,ka amshi takardar nan ka rantsar mata da saki uku a
rubuce' ,abbu yayi caraf yace 'hibba in har kika sa sakin nan ya tabbata
,wallahi zan yafe maki....'',hajiya ce ta karaso tana cewa 'sai dai
'yar taka ta amso maka takardar sakinta,amma aure tsakanin ameera da
bilal,mutu ka raba kofaton doki',sannan hajiya ta cigaba da cewa'ameera
matso kusa da mijinki,in ya tashi tafiya ku wuce tare',meera ta matso ta
dur'kusa a gaban bilal idanunta na zubar da hawaye tana cewa 'dan
Girman Allah mijina,kar ka sakeni,kar ka aikata mini abinda matarka ta
ce ka aikata,ka ji'kaina ka ji tausayina mijina,ka barni da aurenka'
,hannu bilal yasa ya mi'kar da ita tsaye yana cewa 'sssh! Matata,ki
daina asarar hawayenki ,ni dake mutu ka raba,had'in Allah bana mutum
ba,yana da wuyar warwarewa a gun d'an adam',yasa yatsa yana goge mata
hawaye' ,hibbatu kuwa tuni ta nemi hankalinta ta rasa,ta murje
idanunta,ta mintsini kanta amma ko kad'an xuciyarta ba ta daina bata
amsar cewa 'ba mafarki kikeyi ba hibbatullah' ,hannu tasa ta dafe
cikinta da yake murd'awa yana wani 'kugi da hautsinewa, sanadiyar wani
guduwa yake shirin kufce mata,shigowar ammi da ta gaji da jiransu imad a
mota ,yasa hibbatu ta kai duba gareta,ammi tana karasowa kuwa, hibbatu
ta fad'a jikinta ta rungumeta tare 6arkewa da wani irin kuka tana cewa
'nashiga aljanna na zauna daram Ammi,anyi mini FASHIN MIJI! da Makaman
MaKirci'...
Hakkin Mallaka:Abdulaziz ililee Hakkin Mallaka:Abdulaziz ililee isma'il