,_
Ina so ku yi tsokaci a cikin firar da Aisha tayi da Bbc.
BBC: Ko su waye waɗannan mutane da ake zargin sun hana gwamnati rawar gaban hantsi???
Aisha: Kowa ya san su.
BBC: Amma ni ban san su ba.
Aisha: Za ka san su,kar ka damu! Amma kai ta kallon TV za ka gansu da idon ka,idan ka gansu Za ka gane su. Za ka gane ko su waye....
_____________
Amsa ta farko.
Waye MAMMAN DAURA a gurinn Buhari? Shi dai Mamman Daura mutum ne Wanda ke tare da Buhari
Duk da cewa ya girmi Janar Muhammadu Buhari da shekar biyu da rabi, to
amma an bayyana cewa kusancinsu ya wuce yadda ake tunani. Haka kuma
Mamman Daura Kawu ne ga Buhari wanda tun suna da ƙkuruciya suka aminta da juna,
har ta kai komai nasu tare suke yi.
Malam Mamman Daura na girmama juna shi da Buhari wanda ba mai jin cikin su.
A yayin da Buhari ya yiwa Shagari juyin mulki a 1983,
Mamman Daura na ɗaya daga cikin masu ba shi shawara wajen yin hakan. Don haka
Idan har akwai mutumin da Buhari ya ke saurara ya kuma ɗauki shawarar sa ba ya wuce Mamman Daura.
Don haka suka zama tamkar Zara da Wata tsakaninsu,
kusan duk inda ka ga Buhari za ka ga Mamman Daura.
___________________,
Waye ABBA KYARI a gun Buhari?
Sun san juna da Buhari tun a baya, kasancewarsa shima tsohon Soja ne mai tsantseni,
wannan ya taimaka wajen janyo shi fadar shugaban ƙkasa domin amfani da shi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar da zai hana facaka da dukiya.
ABINDA YA FARU DA AISHA.
***
Rahotanni sun ce a baya Mamman Daura ya so haɗa Buhari aure da ɗiyar Sani a nan Zangon Daura, amma hakan bai kai ga faruwa ba.
Lamarin da ya sa Aisha ɗaukar sa a matsayin abokin adawar ta.
***
Ba kamar sauran shugabanni da suka gabata ba
da fadar shugaban ƙkasa ta zama injin ATM da ake shanawa gami da rashawa da dukiyar talakawan ƙkasa.
Daura da Kyari ba su yarda kuɗi su fita haka nan siddam ragadam ba face babu wani dalili.
Wannan ne ya sa Aisha ta ke kallon su a matsayin masu hana ruwa gudu a cikin gwamnatin shugaba Bahari.
***
A yayin ziyarar shugaban ƙkasa zuwa birnin New York kwanakin baya,
ita ma Aisha ta kwashi tawagar mutanen kanta da kuma mai yi mata kwalliya, ta bi bayan sa.
Lamarin da ya janyo kace-nace. Har ta kai shugaban ƙkasa ya shiga kafar sadarwa ya na faɗin ta je ne a karan kanta da kuma kuɗinta.
An ce daga baya Mamman Daura da Abba Kyari sun shaidawa Buhari cewa, "to ya fa sani Aisha na facaka da dukiya dayawa".
Wannan ya sa ya jaddadawa EFCC cewa, idan har suka kama iyalansa da laifi sannan suka raga musu Allah Ya isa bai yafe ba in ji shi Bahari kenan.
A wannan rana ne Aisha ta gamsu cewa,ko shakka babu sun zama ƙkadangarun bakin tulun ta.
Da Gaske su Ba Ƴyan Siyasa Ba Ne?
Kamar yadda Aisha ta faɗa, ba ƴan siyasa ba ne kuma ba su bi Buhari wajen yaƙkin neman zaɓe ba.
Ba kuma lallai ne suna da ƙkuuri'a zabe ba.
Amma Buhari ya kawo su kusa da shi ne domin kada su ci ka da kuma su bari wani ci. Nine naku har kullum wato Musa Rayuwa Jibi.
BUHARI VS AISHA
MUNJI KORAFINKI DUKA MAMA, AMMA DAI GA AMSAR WASU DAGA CIKI:
1.Kina zargin ankyale wasu mutane wadanda aka tura mota dasu, amma aka barsu da hayaki, saidai ana dauko wadanda ko katin zabe basu dashi ana basu mukamai.
AMSARKI MAMA.
*A bayaninki mama na fa'imci ke kina so a kyautatawa wasu mutane wadanda basu wuce miliyan 15 ba, Shi kuma BUHARI yana so ya kyautatawa yan Nigeria miliyan 170 ne. Kinga dole tunaninku yasha banban. A bayaninki mama na fa'imci ke kinaso Idan za'a bada mukami, a duba wadanda suka maida siyasa sana'a, wadanda sukeda yan banga a gidajensu aje, saboda a saka masu abinda sukayi na wahalar siyasa, saboda dama badon kishin kasa sukayi ba, a'a domin a samu a raba. To shi kuma BUHARI yan Nigeria sun bashi amana ne, Idan ya dauki dan siyasa yaba ofishin Phantami, bata dukiyar kasa za'ai, ko kuma idan ya dauki ofishin Hameed Ali na custom, yaba wani yaron Dan siyasa, to dole a saci kudin al'umma aje arabawa yan siyasa, kinga kamar shi yayi kenan. To shiyasa duk mukamai da zai bada a Nigeria saiya duba na kirki, kuma nagari sannan ya bada. Shiyasa ke kanki baki soke shi da zabo mutanen banza ba, saidai kin koka kan ana baiwa marassa katin zabe.
2.Kinyi zargin shi kanshi bai iya gane mutum biyar cikin hamsin wadanda yaba mukamai.
AMSARKI MAMA.
*Wannan Mama ai ya nuna nagartar mijinki sosai, saboda wadanda ya sanin mafi akasarinsu mutanen banza ne, ga irinsu nan muna gani a Majalisar kasa, saboda me zai basu mukamai bayan kuma yasan illarsu, wadanda kike ganin bai saninba, bazai masa wahala ba sanin halayyarsu, saboda yanada iko da DSS ta kasa, kawai zai bada umurni ne a bincika masa PROFILE na Phantami, kwana 2 za'a kawo duk abinda Phantami ya tabayi ko na banza ko na kirki. To kinga ba hujja bace sanin mutum, saidai ko idan anaso acigaba da abinda aka baro baya.
3.Kince kina tsoron bore (rebellion) na mutum miliyan 15 wadanda suka zabeku.
AMSARKI MAMA.
*Mama kin manta a kwai milyan 15 daga yankin Borno, Adamawa, Yobe, su kuma idan goyo kukeso zasu goya ku? Kin manta a kwai irinmu cikin waccan miliyan 15 din, wadanda mun zabekune ba domin ku saka mana ba, saidai don kishin kasa? Kin manta Milyan 15 kashi 1 ne cikin goma na Nigeria, su sauran basuda hakki? Kin manta yan siyasa da kikeso a jawosu atafi dasu, basune suka samar da nasarar mijinki ba, a'a gaskiyarsa ta kwace shi? asalima sun goya dashine suka samu nasara, duk kin manta wannan ne Mama?
4.A karshe kinbada amsar cewa; maganar takarar Baba Buhari, bakuyi magana dashi ba, amma dai ke kin yanke hukunci.
AMSARKI MAMA.
*Mama ni a ganina ai bakida wani hukunci a hannunki, saboda da kina dashi, da masu katin zabe zasu samu mukamai sosai, da irinsu Isa Ali phantami wadanda sukace; su ba yan siyasa bane, bazasu samu mukamiba, sannan kuma da wannan koken naki bazamuji shiba a redio, da saidai kice ga yanda kikeso ayi. Maganar takara kuma, bukatar talakkawa yake dubawa, indai talakka ya kirashi zai amsa kira, inkuma talakka yafi so Barayi su dawo su cigaba da sata, shikenan dama Buhari ya fadi haka. Shi baice dole a sake zabensa ba.
MAGANA TA KARSHE.
*Duk maganarki bata bani mamaki ba, saboda abubuwa kamar haka:
1.An soke office na first Lady
2.Anhana jiragen villa aikinda bana presidency ba, idan mama zata ummara ta hau na haya.
3.Babu mai zuwa zaman fada wurin Mama, domin ya samu mukami ko kwangila
4.Baba baya bada kudi ai shagali, kuma baya son wani yazo ya bada (cin hanci).
5.Ya hana Danginsa zuwa Villa, balle nasu mama.
6.Yace a binciki kowa kasar nan, harda su Mama.
7.Kyautar Kamfuna, Kasashen waje, Ministoci, da yan siyasa duk Baba ya tsaidata.
8.Ko kasan matar Baba, ko baka santa ba, kaidai minene gaskiyar ka.
9.Matan Gwamnoni barayi sunfi matar Baba Hawan motoci da gida.
10.Ya'yan barayin gwamnoni sunfi yayan Mama kudi makudai a Account.
LALLAI DUK ABINDA KAJI YAZO BISA HARSHEN MUTUM, TO SAKON ZUCIYA NE.
Allah ya baki hakuri mama!!
(Buhari ba mijin hajiya bane)
Shidai yace" banzo da komiba Duniya, bazan kuma kwashi kayan kowa ba"
Allah ya baka ikon zuwa lahira saalin aalin.
Daga Jama'a Ne
Title :
Me Ya Sa Mamman Daura,Da Abba Kyari Suka Zama Kishiyoyin Aisha Buhari???
Description : ,_ Ina so ku yi tsokaci a cikin firar da Aisha tayi da Bbc. BBC: Ko su waye waɗannan mutane da ake zargin sun hana gwamnati rawar gaban ha...
Rating :
5