Ministar kudi, Misis Kemi Adeosun ta bayyana cewa kallon da wasu ke yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na wanda bai dauki mata da daraja ba kuskure ne.
Shugaba Buhari dai ya fuskaci suka daga mutane a sassa daban-daban na duniya bayan kalamin da ya yi a kwanan baya cewa aikin matarsa shi ne dafa abinci da kula da turakarsa; abin da ya sa wasu ke yi masa kallon wanda bai dauki mata da daraja ba.
Amma a wata hira da BBC Misis Adeosun ta ce ta yin la'akari da yadda shugaban ya nada mata a manyan mukamai a gwamnatinsa za a fahimci yadda ya dauki mata(da daraja).
''Ina aiki da shi kut-da-kut kuma ban taba ganin ya nuna kaskanci ga mata ba, a ganina ya ma fi bai wa mata fifiko.'' In ji ministar kudin.
Title :
Mata Suna Da Daraja A Wurin Buhari, - Kemi Adeosun
Description : Ministar kudi, Misis Kemi Adeosun ta bayyana cewa kallon da wasu ke yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na wanda bai dauki mata da daraja ...
Rating :
5