Sheikh Bala Lau ya ce "bayan godiya ga Allah da Salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Ya ce "Na saurari jawabin da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi musamman akansa da kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunna. Ya ce "da farko kalmar da Sheikh ya yi a kaina na cewa ni din nan azzalumi ne kuma makaryaci mai daukan mata ya saida su a Saudi Arabia wannan kalma ta batanci da kuma zagi ba zan yi raddi ga wannan Dattijo ba. In zage shi ko in ci mutuncin sa kamar yadda ya ci mutunci na ba".
"Ina lura da shekarun sa a matsayin sa na Uba kuma dattijo amma ina shaidawa Sheikh da duk wanda ya saurari jawabin sa cewa ni ba makaryaci bane, ni ba azzalumi bane kuma ban taba daukan wata mata na je na kai ta kasar Saudi Arabia ba. Allah ya sheda.
"Kuma duk wanda ya san tarihi na a baya to ba haka nake ba. Idan Sheikh Dahiru ya yi amfani da wannan ne don ya ci mutunci na, to ni ba zan mayar mishi da irin kalmar da ya yi akaina ba, lura da matsayin sa na malami. Son haka wannan kalma tashi ba haka nake ba.
"Sannan kuma kungiya ta da ya ce ta nemi hadin kai da su 'yan Dariku don mu yaki 'yan Shi'a, ina tabbatar da wannna babu inda muka taba yin haka da sheikh Dahiru Bauchi koda wani dan Darika. In akwai inda muka taba yin haka a kawo shaida don a tabbatar.
"Kuma kungiya ta ta IZALA ba inda ta kaiwa Kiristoci ko 'yan Darika hari don kashe su ko don kaiwa 'yan Shi'a hari babu wannan.
Sannan har yanzu kungiya ta IZALA ba ta da alaka da Boko Haram.
'Yan uwa musulmai wannan shine takaitaccen abinda zan iya fadi. Ina fata ALLAH S.W.T. ya gafarta mana. ALLAH ya tsare mu daga sharrin shaidan.
"Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu an la'ilaha illah anta astagfiruka wa'atubu ilaika".
Title :
Martanin Sheik Bala Lau Ga Sheik Dahiru Bauchi
Description : Sheikh Bala Lau ya ce "bayan godiya ga Allah da Salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Ya ce "Na saurari jawabin da S...
Rating :
5