Shahararren dan wasan Kannywood Adam A Zango a karo na farko yafito ya bayyana ra'ayin shi akan korar Rahma Sadau da akayi a Kannywood shi dai jarumi yayi magana ne a shifin sa na Instagram...
ga abunda yace daga kasa
'' INA GOYON BAYAN A HUKUNTA RAHAMA SADAU__BANA GOYON BAYAN HUKUNCIN DA AKAYIWA RAHAMA SADAU.
Manzon ALLAH S.A.W tsira da Amincin ALLAH su tabbata agareshi yace. Idan kukaga barna kuyi amfani da bakinku ko dukiyarku ko kuma karfinku wajan hanawa. Don haka masu jin dadin korar rahama da wadan basuji dadi ba. Musani rahama sadau dai yar uwarmuce musulma kuma bahaushiya kuma tayi laifi a addinance da kuma al'adance koda ba'a koreta ba. Dukkammu muna aika laifi wasu a bayyane wasu kuma a boye don haka muyiwa juna adalci wajan fadin gaskiya da bada shawarar arziki a cikimmu yan film da kuma yan kallon fina finan hausa baki daya. Ku roka mata yafiya don a sassauta hukuncin da akayi mata don wadanda suka yanke hukuncin ba mahaukata bane
. ba wai kudinga zage zage ba. Saboda zagi bazai gyara komai ba sai dai ya kara batawa. Idan zagi da cin mutunci zai gyara wani abu daya gyara halin da Nigeria take ciki a yau.
RAMAHA FRIEND DITACE KUMA SHE IS STILL MY BEST FRIEND AMMA HAKAN BAZAI HANA IN FADA MATA GASKIYA BA IDAN TAYI BA DAI DAI BA. ALLAH YA YAFE MANA KURA KURENMU. ''
Title :
Martani Adam A Zango Akan Korar Rahma Sadau Da Akayi A Kannywood
Description : Shahararren dan wasan Kannywood Adam A Zango a karo na farko yafito ya bayyana ra'ayin shi akan korar Rahma Sadau da akayi a Kan...
Rating :
5