Majalisar Dattijai ta tabbatar da nadin Mai Shari'a Ejembi Eko daga jihar Benue da Mai Shari'a Amina A. Augie daga jihar Kebbi a matsayin alkalan kotun koli ta kasa.
Amincewa da nadin ya biyo bayan rahoton da kwamitin shari'a da kare hakkin dan Adam na majalisar karkashin jagorancin Sanata David Umaru ya fitar.
A yayin zaben, Sanatoci 38 cikin 39 sun nuna goyon bayan su ga mai shari'a Eko, yayin da sanata daya ne bai goyi baya ba.
A bangaren mai shari'a Amina kuma, sanatoci 38 ne daga cikin 40 suka mara mata baya.
Title :
Majalisa Ta Tabbatar Da Mutane Biyu A Matsayin Alkalan Kotun Koli
Description : Majalisar Dattijai ta tabbatar da nadin Mai Shari'a Ejembi Eko daga jihar Benue da Mai Shari'a Amina A. Augie daga jihar Kebbi a ma...
Rating :
5