Majalisar Dattawa ta umarci hukumar da ke kula da rundunar 'yan sanda ta kasa(PSC) wadda ke da alhakin daukar aikin dan sanda kan ta dakatar da shirin daukar 'yan sanda har 10,000 wanda ta rigaya ta yi nesa wajen tantance wadanda suka cancanta.
Wata majiya ta nuna cewa matakin majalisar ya biyo bayan sabanin da aka samu ne game da tsarin da hukumar ke bi wajen daukar aikin dan sandan na raba guraben ta hanyar jihohi a maimakon baiwa kowace karamar hukuma na kasar nan gurbinta kamar yadda tsarin daukar aiki na kasa ya tanada.
A cewar majiyar, a bisa tsarin doka, hukumar PSC na da ikon daukar manyan jami'an 'yan sanda ne na matakin ASP a yayin da rundunar 'yan sanda ta kasa ke da alhakin daukar kananan jami'ai. Sai dai hukumar ta PSC ta nuna cewa ba ta dakatar da aikin daukar 'yan sandan ba.
Title :
Majalisa Ta Nemi A Dakatar Da Shirin Daukar Aikin Dan Sanda
Description : Majalisar Dattawa ta umarci hukumar da ke kula da rundunar 'yan sanda ta kasa(PSC) wadda ke da alhakin daukar aikin dan sanda kan ta da...
Rating :
5