Ma’aikatan ‘yan majalisar tarayya sunyi zanga-zangar limana a cikin majalisar a jiya 25 ga watan Oktoba, sakamakon kin biyansu kudin alawus alawus dinsu.
Ma’aikatan ‘yan majalisan wa’anda basuda yawa sun nuna rashin jin dadinsu ne bayan da aka ki biyansu alawu dinsu na tsawon shekara daya da wata hudu.
Haka kuma suna mamakin cewar anyi musu alkawari za’a biyasu kudaden nasu domin kuwa an sanya kudin a cikin kasafin kudi na shekarar 2015 dakuma 2016 amman har yanzu basuga komai ba.Haka kuma, ma’aikatan suna korafi ne akan abubuwa guda biyu.
1. Kin biyansu albashi akan lokaci.
2. Sannan kuma kudin tara da ake cire musu a albashin su.
3. Rashin zuwa karo ilimi.
Haka kuma jami’an ‘yan sanda sun shiga tsakani dangane da zanga-zangar.
Naij Hausa
Title :
Ma'aikatan 'Yan Majalisa Sunyi Zanga-Zanga A Majalisa
Description : Ma’aikatan ‘yan majalisar tarayya sunyi zanga-zangar limana a cikin majalisar a jiya 25 ga watan Oktoba, sakamakon kin biyansu kudin alawus ...
Rating :
5