Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta yi amai ta tande, inda yanzu ta bukaci dakatar da Alkalan da ake zargi da karbar cin hanci har sai an kammala bincike ko wanke su a gaban kotu. Shugaban kungiyar Abubakar Mahmud wanda a farko ya bayyana kafa dokar ta-baci dangane da kama alkalan, ya ce ya sauya matsayisa ne dan kare martabatar sana’ar.
Mahmud ya bukaci dakatar da wadanda ake zargin da kuma ba su damar wanke kansu daga tuhumar da ake musu.
Yanzu haka ana ci gaba da samun manyan masana shari’a da ke ci gaba da bayyana goyan bayansu na tsaftace bangaren shari’ar a Najeriya.
A makon da ya gabata ne dai hukumar tsaron farinya DSS ta yi dirar mikiya a gidajen wasu manyan alkalan kasar da suka hada da na kotun koli da na babbar kotu a wasu jihohin kasar.
DSS ta ce jami’an sun samu miliyoyin kudi a gidajen alkalan da ake zargi sun karbi cin hanci.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce fada ne da rashawa amma ba akan bangaren shari’a ba.
Madogara RFI Hausa
Title :
Kungiyar Lauyoyi Najeriya Ta Yi Amai Ta Lashe
Description : Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta yi amai ta tande, inda yanzu ta bukaci dakatar da Alkalan da ake zargi da karbar cin hanci har sai an kammala ...
Rating :
5