An Yanke Wa Tsohon Shugaban Karamr Hukuma Shekaru 70 A Gidan Yari
Mahmud Isa Yola
Kotun daukaka kara na tarayya a Yola ta yanke hukuncin shekaru saba'in a gidan yari ga tsoho shugaban karamar hukuman Hong na jihar Adamawa a bayan ta same shi da laifin almundahana da dukiyar gwamnati.
Wannan yana kunshe ne a cikin wani rahoto da hukumar EFCC ta fitar inda rahoton ya bayyana cewa a ranar shida ga watan nan ne Alkali B. B Aliyu na kotun daukaka kara dake Yola, ya tabbatar da kama tsohon shugaban karamar hukuman Ibrahim Buba Gayus, tare da tsohon jami'in kudi na karamar hukumar da laifin sama da fadi da kudi naira miliyan arba'in daya da dubu dari daya (N41.1).
Rahoton ta tabbatar da cewa a shekarar 2015 ne aka fara tuhuman Ibrahim Gayus da laifin karban kudi naira miliyan hamsin rance na noma a madadin karamar hukumar amma sai ya bada naira miliyan goma bayan ya amshi kudin ya rike saura.
A sabida haka ne Alkali Aliyu Aliyu ya yanke hukunchin shekara bakwai akan kowani laifi cikin laifuka goma da aka samu tsohon shugaban karamar hukumar da su.
Amma mai tsare masu laifuka Isreal Akande ya nemi kotun ta bada dama ga mai laifin ya dawo da kudin.
Kotun ta amsa kokon baran inda ta umurci mai laifin ya dawo da kudin asusun karamar hukumar Hong.
Title :
Kotu Ta Yanke Hukunci Shekara Saba'in Ma Wani Tsohon Shugaban Karamar Hukuma
Description : An Yanke Wa Tsohon Shugaban Karamr Hukuma Shekaru 70 A Gidan Yari Mahmud Isa Yola Kotun daukaka kara na tarayya a Yola ta yanke hukuncin ...
Rating :
5