A wani mataki na cike gibin man da Nijeriya ke samarwa, Kamfanin Mai Na Kasa( NNPC) ya kara kaimi wajen aikin hako mai a tafkunan Chadi da na Benue wanda ake sa ran adana man da hako don amfani da shi don gaba.
Da yake karin haske kan batun, Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya tabbatar da cewa an fara samun nasara a aikin hako mai inda ya nuna cewa kamfanin zai yi amfani da sabbin fasahar zamani don ganin an cimma bukata cikin gaggawa.
A watan Yuli ne dai Shugaba Buhari ya ba kamfanin NNPC umarnin gaggauta fara aikin hako mai a tafkunan Chadi da Benue don ganin an maye gibin da ake samu na yawan mai da Nijeriya ke samu wanda ya ragu matuka sakamakon ayyukan mayakan kungiyoyin tsagerun Niger Delta.
Title :
Kamfanin NNPC Ya Fara Samun Nasara Wajen Aikin Hako Mai A Arewa
Description : A wani mataki na cike gibin man da Nijeriya ke samarwa, Kamfanin Mai Na Kasa( NNPC) ya kara kaimi wajen aikin hako mai a tafkunan Chadi da ...
Rating :
5