"
Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya nemi gwamnatin shugaba Buhari da ta rabu da shi ta mayar da hankali halin ha’ula’in da jama’a ke ciki.
A wata jawabin da mai Magana da yawunsa ya sanya hannu. Lere Olayinka, gwamnan yace hukumar EFCC ta ci gaba da guje-gujen ta, ba zai daina gudanar da shugabanci mai kyau ga mutanen jihar Ekiti ba.
Fayose yace : “Mun wuce wannan zancen, EFCC ta daina wahala, sunyi fiye da haka a 2006,kuma gashi yau ina gwamna, Idan wannan shi ne dalilin da yasa suke yaki da Alkalai da shari’a, bazasu iya mini ba, ina nan ina ma mutanen jihar Ekiti aiki "Obanikoro dai ya mika kansa ne ga hukumar EFCC a ranan litinin 17 ga watan oktoba,akan badakalar kudin makaman da ya amsa N4.745billion daga hannun Sambo Dasuki.
Kuma yace ya baiwa Fayose N2.23billion daga cikin kudin.
A ranan 17 ga watan oktoba ne gwamna Ayodele fayose ya hana jami’an yan sanda damke uwargidan Femi Fani Kayode da laifin cire kudin gwamnati a banki.
Title :
Ka Rabu Da Ni Ka Ceci 'Yan Nijeriya" Fayose Ya Kalubalanci Buhari.
Description : " Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya nemi gwamnatin shugaba Buhari da ta rabu da shi ta mayar da hankali halin ha’ula’in da jama’...
Rating :
5