A wani mataki na wanke kansa, tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya yi ikirarin cewa sai da ya gargadi Goodluck Jonathan game da yadda gwamnatinsa ke salwantar da kudaden gwamnati, lamarin da ya janyo Nijeriya ta tsinci kanta cikin wannan yanayin kuncin rayuwa.
Tsohon Shugaban ya bayyana haka ne a garin Abeokuta inda ya nuna cewa Jonathan ya ki bin shawarar da ya bashi wanda a kan haka a yau, ana fama da rashin aiki a tsakanin matasa wanda a cewarsa, Babban matsala ce wadda ke iya haifarwa kasar nne wani sabon fitina.
Rariya
Title :
Jonathan Ne Ya Jefa Nijeriya Cikin Halin Kunci - Obasonjo
Description : A wani mataki na wanke kansa, tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya yi ikirarin cewa sai da ya gargadi Goodluck Jonathan game da y...
Rating :
5