Shugaban Jami’ar ABU Zaria, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Jami’ar ta ABU Zaria na shirin jan wutan lantarki daga dattin bola da ake samu a gonaki da gidaje. Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana wannan ne a farfajiyar makarantar da ke Samaru-Zaria.
Farefesa Garba yace Jami’ar za tayi haka ne domin kudin da ta ke kashewa a wajen shan wutan lantarki yana da matukar yawa, Jami’ar ABU Zaria tana dai kashe akalla Naira Miliyan 86 kowane wata wajen biyan kudin wuta kadai, wanda kuma ba za ta iya cigaba da biya ba Inji Farfesa Ibrahim Garba.
Jami’ar za ta hada kai da wani Kamfanin Kasar Hungary mai suna Agrar-Biothanal, wajen gina mabubbugar wuta daga dattin bolar da ake samu daga gonaki da kuma sauran wurare irin su ba-haya. Idan har an kamalla wannan aiki, Farfesa Garba yace za a samu kusan lita miliyan uku na Sinadarin Ethanol, da kuma ruwan taki fiye da ton dubu, sannan da megawatt 1.2 na lantarki.
Jakadan Kasar Hungary a Najeriya, Farfesa Temak Gabor yace dole Najeriya ta fara neman wasu hanyoyin samun wutar lantarki saboda yawan da ta ke da shi. Makon baya ne dai gwamnatin Kano da Kaduna suka hada kai wajen irin wannan aiki na samun wutan lantarki.
Title :
Jami’ar ABU Zaria Za Ta Samar Da 1.2MW Daga Ba-haya
Description : Shugaban Jami’ar ABU Zaria, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Jami’ar ta ABU Zaria na shirin jan wutan lantarki d...
Rating :
5