Ana sa ran Goodluck Jonathan ya zo kotu domin yin shaida ga Sambo Dasuki bayan yace bai yarda cewa Dasuki ya sace $2.2 billion badakalar kudin makamai
Dasuki ya kasance a tsare bayan an tuhumesa da laifin karkatar da kudin makamai inda ya rabawa yan jam’iyyar PDP da dama.
Kana, tsohon shugaban kasa yayinda yake magana a ranan litinin ,24 ga watan oktoba a Oxford Union yace bai yarda da cewa Dasuki ya sace $2.2 billion saboda sun sayi jiragen yaki da kuma makamai.
Yace “Ban yarda cewa wani zai iya sace $2.2 billion, mun sayi jiragen ruwa, jiragen yakin sama, makamai da dama da sauran su kuma kuna cewa $2.2 billion, shin da wasu kudade aka sayi wadannan abubuwa.”
Wannan magana ya ja hankalin lauyoyin dasuki ku suna sa ran gayyatar sa domin yin shaida ga Sambo Dasuki.
Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa, Mr. Ahmed Raji ,lauyan Dasuki yace yana son Jonathan yayi shaida a kotu. Yace: “Zamu so Jonathan yay i shaida akan Dasuki . wanna zai taimaka matukakuma zai taimaka wajen yin adalci.”
Title :
Ina Son Jonathan Yayi Mini Shaida A Kotu - Dasuki
Description : Ana sa ran Goodluck Jonathan ya zo kotu domin yin shaida ga Sambo Dasuki bayan yace bai yarda cewa Dasuki ya sace $2.2 billion badakalar kud...
Rating :
5