Tsohon shugaban kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN a Nijeriya, Alhaji Sani Mu'azu Jos, Daraktan kamfanin Lenscope Media ya bayyana goyon bayan sa da korar karen da aka yi wa jaruma Rahama Sadau daga harkar shirya finafinan Hausa, sakamakon abin badalar da ta aikata, wanda bai yi wa masana'antar shirya finafinan Hausa dadi ba.
Alhaji Sani Mu'azu, wanda jigo ne a harkar shirya finafinai ba kawai a Arewacin Nijeriya ba har ma da kudanci, ya yi nuni da cewa abin da jaruma Rahama Sadau ta aikata babban abin takaici ne ganin cewa wannan ba shi ne karon farko da take aikata abubuwan da suke sabawa dokoki da ka'idojin kungiyar ba.
Ya ce, sau biyu ana dakatar da ita daga harkar shirya finafinan, saboda abubuwan da take aikatawa da ba su dace ba, amma daga baya sai ta dawo ta nuna nadama ta ba da hakuri. Har dai a karshe ta rubuta takardar karshe ta rantsuwar ba za ta sake aikata abin da ya sabawa ka'idojin kungiyar ba.
"Abin da shugabannin MOPPAN na yanzu suka aikata na korar Rahama baki daya daga industirin Hausa ya yi daidai, kuma hakan zai kara taimakawa wajen kara gyara harkar da take cigaba da shan suka daga bangarorin al'umma daban daban, sakamakon kurakuran da wasun mu ke aikatawa."
Ana zargin jaruma Rahama Sadau ne dai laifin nuna halayyar da ba ta dace ba, a cikin wata wakar soyayya da wani mawaki dan Jos, mai suna ClassiQ ya sa ta a ciki, inda ta taka rawar da ta jawo mata tofin alatsine daga jama'a.
Zuma Times Hausa
Title :
Ina Goyon Bayan Korar Rahama Sadau... In Ji Sani Mu'azu
Description : Tsohon shugaban kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN a Nijeriya, Alhaji Sani Mu'azu Jos, Daraktan kamfanin Lenscope Media ya ...
Rating :
5