Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah, Malam ya hidima da ake tayi damu dalibai, Allah ya saka da alkhairi. Allah ya albarkaci Zuri'a, Amin.
Malam Nayi dahara da ruwan da nayi wanka dashi da niyyar idan na fito zan Kuma yi da wani ruwan daban. Dana fito sai na manta har nayi sallar azahar da laasar, Sai na tuna da magriba. Malam ya zanyi na gyara. Bissalam.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hukuncin ya danganta da irin yanayin ruwan wankan. Idan ruwan wankan sabulu ne, Kuma ya riga ya chakude da sabulun, to lallai wannan tsarkin naka bai yiwu ba. Kuma zaka rama dukkan sallolin da kayi da wannan tsarkin.
Amma idan wankan ibadah kayi, ko kuma wankan sanyaya jiki, to ya halatta kayi tsarki da irin ragowar ruwan wadannan wankan. Mutukar dai siffofinsa basu chanza ba.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 19-10-2016 (17-01-1438).
Title :
HUKUNCIN YIN TSARKI DA RUWAN WANKA
Description : Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah, Malam ya hidima da ake tayi damu dalibai, Allah ya saka da alkhairi. Allah ya albarkaci Zuri'a, Amin. ...
Rating :
5