...Babu Mai Hana Mu Sakin Hirar Saidai..., Inji BBC
Rahotanni sun nuna cewa fadar gwamnatin tarayya na yunkurin hana kafar yada labarai ta BBC Hausa fitar da hirar da suka yi da uwargidan shugaban kasa A'isha Buhari, inda ake ganin ta bi sahun wasu daga cikin al'ummar kasar nan wajen suka gwamnatin mijin nata.
Majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito cewa baya ga shugaban kasa da sauran mukarrabansa na fadar gwamnati da suke kokarin ganin an dakatar da fitar da hirar, shi ma kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Yakubu Dogara da wasu daga cikin wasu makusanta shugaba Buhari suna iya kokarin su don ganin BBC ba ta fitar da hirar ba.
Sadai a gefen kafar yada labaran ta BBC kuma, ta bayyana cewa a matsayinta na kafar yada labarai mai zaman kanta babu abinda zai hana fitar da hirar saidai idan ita uwargidan shugaban kasar da aka hira da ita din ne ta bukaci kada a saki hirar.
Hirar wadda BBC za ta fitar a gobe Juma'a, A'isha Buhari ta bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda mijinta ya baiwa mukamai ba su yi wa jam'iyyar APC wahala ba, yayin da kuma aka bar wadanda suka yi wahala a gefe ba tare an ba su mukamai ba.
Kuma ana ganin a ragowar hirar matar shugaban kasan ta soki gwamnatin mijin nata fiye da yadda ake tsammani. Domin har sai da ta kai ga ta bayyana cewa ba ta tunanin mijinta zai sake samun adadin kuri'u milyan 15 da ya samu a zaben 2015 idan ya kudiri aniyar sake fitowa takara a 2019.
Rariya
Title :
Gwamnati Tarayya Na Neman Hana BBC Sakin Hirar Da Ta Yi Da Uwargidan Shugaban Kasa
Description : ...Babu Mai Hana Mu Sakin Hirar Saidai..., Inji BBC Rahotanni sun nuna cewa fadar gwamnatin tarayya na yunkurin hana kafar yada labarai ta ...
Rating :
5