Shafin sada zumunta na Facebook ya kara harsuna uku, da suka hada da Fulatanci a cikin harsunan da mutane za su iya amfani da shafin.
Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg wanda ya sanar da hakan ya ce yanzu akwai harsuna sama da dari kenan da ake amfani da su a shafin.
Mista Zuckerberg ya ce akwai fiye da mutane biliyan daya a duniya dake amfani da wani harshe daga a shafin na Facebook daga cikin harsunan wanda kuma ba Turanci ba.
“A kun kara harsunan Fulatanci da Malte da akafi amfani da shi a kasar Malta, da kuma harshen Corsica da aka fi amfani da shi a yankunan kasar Italiya. Hakan ya yiwu ne da taimakon mutanen dake amfani da shafin Facebook”, Inji Zuckerberg.
Ya ce a cikin shekaru goma da suka wuce, dubban mutane sun taimaka wajen fito da fassarar kalmomi da jumloli da za a iya amfani da su a Facebook.
Harshen Fulatanci da aka kara a shafin na Facebook, ana amfani da shi sosai a Najeriya, musanman a arewa maso gabashin kasar, da ma wasu kasashe kimanin ashirin a yammaci da tsakiyar Afirka.
A baya shafin na Facebook ya sanya harshen Hausa, sannan ya sha alwashin kara wasu harsunan domin ba jama’a damar yin mu’amala da wadanda suke so cikin sauki.
Title :
Facebook Ta Sanya Fulatanci A Cikin Harsunansa
Description : Shafin sada zumunta na Facebook ya kara harsuna uku, da suka hada da Fulatanci a cikin harsunan da mutane za su iya amfani da shafin. S...
Rating :
5