Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta garkame gidan tsohon Gwamnan Bauchi a karkashin jam'iyyar PDP, Malam Isah Yuguda.
EFCC ta rufe ginin wanda ke kan titin Sir Kashim Ibrahim Street, a GRA Bauchi ne da yammacin Asabar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai taimakawa Gwmnan Bauchi kan sabbin kafafen yaɗa labarai Alhaji Shamsudeen Lukman Abubakar ya ce, "ba mamaki rufe gidan baya rasa nasaba da irin ɗimbin takardun koke ne da Gwamna mai ci a yanzun Muhammad Abubakar ya rika aikawa hukumar EFCC kan cewa su binciki tsohon Gwamnan."
Ana dai zargin Isah Yuguda da yin wadaka da dukiyar jihar Bauchin a lokacin Gwamanatinsa.
Title :
EFCC Ta Soma Bincikar Tsohon Gwamnan Bauchi Isah Yuguda
Description : Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta garkame gidan tsohon Gwamnan Bauchi a karkashin jam...
Rating :
5