An nada babban mai ruwa da tsaki a harkar finafinan Hausa, Ibrahim Muhammad Mandawari, a matsayin mai unguwar Mandawari, da ke cikin birnin Kano.
A ranar 7 ga watan Oktoba ne dai aka tabbatar da nadin a gaban hakimin Dala, sannan kuma Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sunusi na biyu ya amince da nadin.
Ya gaji mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Auwalu Shawai, wanda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daya ya nada, a zamaninsa.
Ya gaji mahaifisan sa a matsayin mai unguwar Mandawari.
Ibrahim Mandawari dai na daga cikin mutanen da suka assasa harkar finafinan Hausa ta zamani a da ake kira Kannywood.
Ya shedawa BBC cewa zai ci gaba da shiryawa da kuma fitowa a finafinan Hausa irin wadanda ya saba fitowa a baya.
'Yan uwa da abokan arziki dai sun taya shi murna bisa wannan nadin na sa.
Ya kuma shaidwa BBC cewa ya yi matukar farin ciki da wannan nadi da aka yi masa da ya gaji mahaifinsa.
Title :
Duk Da Cewa Na Zama Mai Unguwa Amma Zan Ci Gaba Da Fita A Finafinai - Ibrahim Mandawari
Description : An nada babban mai ruwa da tsaki a harkar finafinan Hausa, Ibrahim Muhammad Mandawari, a matsayin mai unguwar Mandawari, da ke cikin birnin...
Rating :
5