Mawakin da ya sanya jaruma Rahma Sadau a bidiyon da ya janyo cece kuce wato Classiq ya bayyana cewa bai ji dadin hukuncin da hukumar kula da finafinan Hausa ta yankewa jarumar.
A hirar sa da jaridar Premium Times, mawakin ya bayyana cewa “Ni na roki Rahama Sadau da ta fito a bidiyo na saboda ita fittacciya ce a masana’antun nishadi, ba wai don wani abu ba. Na sa tane saboda ina son fittacciyar fuska a bidiyon,”. “Tun daga lokacin Lokacin ba cece kuce ya biyo bayan fitowar bidiyon, na kasa samun sukuni domin ban yi tsammanin abin zai kai haka ba. Na yi juyayi kan korar nata. Har yanzu ina jin wannan yanayi a ce an koreta daga masana’anta saboda ta fito a
bidiyona.
Classiq ya kuma kara da cewa Rahama Sadau mutuniyar kirki ce.
Title :
Dalilin Da Ya Sa Na Sanya Rahma Sadau A Bidiyon Wakata, - Classiq
Description : Mawakin da ya sanya jaruma Rahma Sadau a bidiyon da ya janyo cece kuce wato Classiq ya bayyana cewa bai ji dadin hukuncin da hukumar kula d...
Rating :
5