Mawakin nan mai suna Classiq wanda ya yi waka tare da rungume-rungume da Rahma Sadau, ya ce, yana neman afuwar jarumar.
Mawakin, a shafinsa na Instagram, ya ce “fitowar faifan wakarsa da ya yi wa lakabi da ‘i love you’ ta jawo kace-nace.”
A saboda haka ne Classiq ya ce ” zan so na nemi gafarar Rahma Sadau saboda irin halin da wakata ta jefa a ciki.”
Classiq ya kara da neman afuwar masoya Rahama Sadau.
To amma mawakin ya bayyana jarumar da mai hazaka da jajircewa, a inda ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kasancewa tare da Rahma Sadau.
A ‘yan makonnin da suka gabata ne dai kungiyar masu hada fina-finan Hausa wato MOPPAN, ta sanar da korar Rahma Sadau daga harkokin fim.
Title :
CLASSIQ Ya Nima Gafarar Rahma Sadau
Description : Mawakin nan mai suna Classiq wanda ya yi waka tare da rungume-rungume da Rahma Sadau, ya ce, yana neman afuwar jarumar. Mawakin, a shafinsa...
Rating :
5