Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya ba wa Babban sufeton 'yan sanda na kasa Ibrahim Idris umarnin bincikar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, akan zargin karbar cin hancin Naira Miliyan 500 da aka ce ya karba a hannun kamfanin sadarwa na MTN.
A baya dai wasu kungiyoyi sun yi korafin cewa, babban sufeton 'yan Sandan ba zai iya bincikar Abba Kyari ba, kasancewar ya taka Muhimmiyar wajen nada shi zuwa matsayin da ya ke. Wannan binciken ya zo kwanaki bayan matar shugaban kasa Aisha Buhari ta yi korafin sun kankane mijinta sun hana shi rawar gaban hantsi.
Title :
Buhari Ya Bayar Da Umarnin Bincikar Abba Kyari
Description : Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya ba wa Babban sufeton 'yan sanda na kasa Ibrahim Idris umarnin bincikar shugaban ma'aikatan ...
Rating :
5