Shugaba Muhammad Buhari ya ba hukumar EFCC umarnin ta binciki duk wani daga cikin iyalansa wanda ake zargi da aikata laifin rashawa inda ya nuna cewa ba zai taba yafewa hukumar ba idan har ta ki bin wannan umarni.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin sabon littafin tarihin Shugaban wanda Farfesa John Paden ya rubutu inda a cikin littafin aka nuna cewa Shugaba Buhari ya ki amincewa da matsim lamba kan ya dakatar da binciken da ake yi wa wasu jigogin jam'iyyar APC kan rashawa.
An nuna cewa Shugaba Buhari ya sha nanata cewa ko da 'ya'yansa ne aka samu da aikata laifin rashawa, to gaggauta hukunta su, matakin da ya kara ba Shugaban EFCC karfin guiwar aiwatar da aikinsa ba tare da wani fargaba ba.
Title :
Buhari Ya Ba EFCC Umarnin Binciken Iyalansa
Description : Shugaba Muhammad Buhari ya ba hukumar EFCC umarnin ta binciki duk wani daga cikin iyalansa wanda ake zargi da aikata laifin rashawa inda ya...
Rating :
5