Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Jamila Nagudu ta shaida wa BBC cewa ba ta da saurayi a cikin masu yin fina-finan.
Sai dai ta kara da cewa idan ta gamu da wanda ranta ke so a cikin abokan aikinta ba za ta yi kasa-a-gwiwa wajen aurensa ba.
Fitacciyar jarumar ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa ‘yan fim cewa ba sa son yin aure, tana mai cewa “idan lokacin yin auren mutum bai yi ba babu yadda za a yi ya yi da kansa”.
A cewarta, “Mutanen da suke cewa ba ma son zaman aure, su dubi sauran al’umma mana. Akwai mata da yawa wadanda suka girme ni amma ba su da aure saboda Allah bai sa lokacin yinsu ya yi ba.”
Title :
Photos:Bani Da Wani Saurayi – Jamila Nagudu
Description : Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Jamila Nagudu ta shaida wa BBC cewa ba ta da saurayi a cikin masu yin fina-finan. Sai d...
Rating :
5