Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya sake nuna shakka game da satar fiye da ‘Yan matan makarantar gwamnati ta mata ta garin Chibok 200 da akayi cikin Aprilu 2014 a jihar Borno. Yace har yanzu bai yarda an sace yaran ba domin ana yin abubuwa a asirce. Gwamnan ya fadi haka a wani shiri da gidan talabishin na Channels mai suna Hard Copy ranar Juma’a 21 ga Oktoba
Yace: “Ina cikin duhu game da ‘yan matan Chibok. Fiye da dalibai 200 zasu je yin jarrabawa kan kimiyya. Zasu yi jarrabawa kan kimiyya amma ta farko da suka kawo bata iya magana da harshen Ingilishi, yayin da ta biyu gungun ‘bring back our girls’ suka kangeta. In ka kalli abinda ya faru sai ka fara tambaya shin wannan gaskiya ne kusa?”
naij Hausa
Title :
Ban Yarda An Sace 'Yan Matan Chibok Ba - Fayose
Description : Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya sake nuna shakka game da satar fiye da ‘Yan matan makarantar gwamnati ta mata ta garin Chibok 200 da...
Rating :
5