Sarkin Kano Muhammadu SANUSI ya karyata rade-radin da ake ta yi cewa wai ya maida wa Sarkin Katsina Abdulmumini martani akan aurar da wata yarinya yar shekara 14 mai suna Habiba da yayi.
Sarkin Kano ya ce bashi da shafin Sadarwa na Facebook ko Twitter in da ake ta yadawa wai ya fadi hakan.
Ya ce suna da kwakkwaran zumunci tsakanin masarautar sa da na Katsina saboda haka idan har akwai bukatar su tattauna akan wani abu zuwa zai yi ba ta shafin yanar gizo ba.
Source Premium Times Hausa
Title :
Ban ce komai ba akan auradda Habiba da Sarkin Katsina yayi - Sarkin Kano
Description : Sarkin Kano Muhammadu SANUSI ya karyata rade-radin da ake ta yi cewa wai ya maida wa Sarkin Katsina Abdulmumini martani akan aurar da wata ...
Rating :
5