Fitaccen mai bayar da umarni a finafinan Hausan nan, Sanusi Oscar wanda aka fi sani da 4-4-2, ya bayyana cewa ba za su taba amincewa wata kungiya daga gefe ta yi yunkurin korar musu jarumi kamar Ali Nuhu a masana'antar fim ba.
Sanusi Oscar, wanda shine kakakin kungiyar 'yan fim na Arewa (AFMAN), ya kara da cewa Ali Nuhu memba ne a kungiyar su don haka su suke da alhakin su yi masa hukunci a duk lokacin da ya aikata wani laifi.
Darakta Oscar dai ya bayyana hakan ne biyo bayan kalaman da sakataren kungiyar masu shirya finafinai na kasa (MOPPAN), wato Salisu Oficcer ya yi na cewa koda Ali Nuhu ne ya aikata irin laifin da Rahma Sadau ta yi, za su kore shi daga masana'antar.
Ya ce shi bai ga laifi ba don Ali Nuhu ya fadi ra'ayinsa game da hukuncin da aka yankewa Rahma Sadau wannda har zai kai ga cewa MOPPAN ta mayar masa da martani idan har bada wata manufa suka yi masa martanin ba.
Oscar ya kara da su kungiyar su ta AFMAN tana da tsari wajen hukunta dan fim idan ya yi laifi, kuma sukan yi masa hukunci ne cikin sirri ba tare da sun tozarta shi a idon duniya ba.
Oscar ya kuma zargi kungiyar ta MOPPAN da yunkurin rusa masana'antar fim din Hausa, domin a cewarsa kungiyar ta sanyawa wasu hazikan jaruman fim maza da mata ido. Wanda kuma idan babu wadannan jarumai a farfajiyar fim, to masana'antar fim ta mutu.
Oscar ya kara da cewa kungiyar AFMAN ita ce garkuwar masana'antar fim domin duk wasu ci gaban da ake samu a Kanneywood ita ce sila. Inda ya kawo misali da yin hanyar daukar nauyin wasu 'yan fim zuwa karo ilmi kasar waje a kwanakin baya da kuma karbo bashi daga gwamnatin tarayya domin bunkasa masana'antar da kungiyar ta yi. Ya ce don haka babu wata kungiya da za ta zo daga baya ta yi wa masana'antar finafinan Hausa katsalandan.
A game da hukuncin korar Rahma Sadau daga masana'antar fim da kngiyar ta MOPPAN ta yi, Oscar ya bayyana cewa "hukuncin ya yi tsanani, duk da cewa ba za mu ce komai ba saboda Rahma Sadau ba membanmu ba ce saboda ba ta yi rijista da AFMAN ba".
Oscar ya kuma ja hankalin sauran jaruman finafinan Hausa da su kasance masu tsoron Allah don ganin sun kaucewa duk wani abin da zai iya jawo sabawa dokokin addininsu na musulunci da zubewar mutuncinsu a idon duniya.
Rariya
Title :
Ba Za Mu Bari Wata Kungiya Ta Ci Zarafin Ali Nuhu Ba, - Sanusi Oscar
Description : Fitaccen mai bayar da umarni a finafinan Hausan nan, Sanusi Oscar wanda aka fi sani da 4-4-2, ya bayyana cewa ba za su taba amincewa wata k...
Rating :
5