Idan Gwamnatin Buhari Ta Ci Gaba Da Tafiya A Haka
Rikicin Jam'iyyar APC na daukar sabon salo. Rahotanni sun nuna cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fara kulla wata alaka tsakanin sa da jigo a Jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, domin neman mafita a babban zaben 2019, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
Sai dai ana fargabar wannan alaka za ta iya wargaza Jam'iyyar APC sakamakon fara tunanin kirkirar sabuwar Jam'iyya da suke yi.
Jaridar ta jiyo daga kwakkwarar majiya ta Jam'iyyar APC cewa, "Tinubu na kwakkwaran shiri tsakanin sa da Atiku na ficewa daga Jam'iyyar tare da gungun masoyansu matukar Buhari ya ci gaba da tafiyar da shugabanci a yadda ya ke yi yanzu".
Rariya
Title :
Atiku Da Tinubu Na Shirin Kirkiro Sabuwar Jam'iyya
Description : Idan Gwamnatin Buhari Ta Ci Gaba Da Tafiya A Haka Rikicin Jam'iyyar APC na daukar sabon salo. Rahotanni sun nuna cewa, tsohon mataimaki...
Rating :
5