An toshe hanyoyin sadarwa na intanet a Habasha a daidai lokacin da 'yan kasar ke cigaba da zanga-zangar adawa da gwamnati.
Ba a dai bayar da dalilin toshe intanet din a hukumance ba.
A baya dai gwamnati ta zargi 'yan kasar, masu adawa wadanda ke zaune a kasashen waje da yin amfani da kafafen sada zumunta na Facebook da Twitter wajen shirya zanga-zanga a kasar.
Ko a watan Agusta ma sai da aka toshe damar amfani da intanet a lokacin wata zanga-zanga da aka yi.
Akalla mutum 55 ne suka rasa rayukansu a wani turmutsutsu a wurin wani bikin al'ada a yankin Oromia a ranar Lahadi.
Kungiyoyin 'yan adawa sun zargi jami'an tsaro da budewa mutanen da ke zanga-zangar wuta abin da a cewarsu ya jawo turmutsutsun.
Sai dai Firai Minista Hailemariam Desalegn, ya musanta zargin, inda ya ce, masu zanga-zangar ne suka haddasa rikicin da ya janyo mutuwar mutane da dama.
Title :
An Toshe Intanet A Kasar Ethiopia
Description : An toshe hanyoyin sadarwa na intanet a Habasha a daidai lokacin da 'yan kasar ke cigaba da zanga-zangar adawa da gwamnati. Ba a dai bay...
Rating :
5