A safiyar yau ne mabiya Shi'a suka fito domin gudanar da Muzahara amma hakar su bata cimma ruwa ba inda suka sha barkono mai sa hawaye.
Haka makamancin haka ya auku a yanzu haka a masallacin Fagge dake cikin birnin Kano, inda jami'an sanda suka dinga har barkonon tsohuwa sama.
Saida babu tabbacin ko akwai wadanda suka ji rauni ko suka rasa ransu.
Idan baku manta ba a 'yan kwanakin nan ne yan Shi'a sun samu kalubale daga wasu jahohi har kamar Kaduna, Kano da Katsina.
Rariya
Title :
An Tarwatsa Dandazon Mabiya Shi'a Da Suke Mazahara A Jihohin Kano Da Katsina
Description : A safiyar yau ne mabiya Shi'a suka fito domin gudanar da Muzahara amma hakar su bata cimma ruwa ba inda suka sha barkono mai sa hawaye....
Rating :
5