Hankali ya tashi matuka da bayyanar wani shafi mai suna kasuwar mata da wasu lalatattun matasa suka bude suna dauko hoton matan mutane suna tallata su da sunan ma su neman aure ko sugar Mommy's. Cikin ikon Allah an samu wani masani a harkar binciken kwakwaf akan sanarwar zamani wato Social Media and Internet Intelligence daga makarantar London Film Academy Mr Ardo Jagordo Fulbe ya binciko cewa wani matashi ne mai Suna Zahradeen Ahmad ya bude shafin ranar 12-Sept-2016 misalin karfe 3:18. Binciken ya bayyana sunaye da lambobin akalla mutum goma da lambobin wayar su, kuma an gano yawancin su yara ne kanana suke wannan aika-aika. Sheriff Almuhajir ya ce "Abinda ya fi bani mamaki shine duka duka shafin bai kai wata guda ba, amma ya samu followers akalla mutum dubu ashirin da shida. Abokai na cikin su mutum 125 ne. Har da su wa'e da wa'e. Muna fata za su gaggawar rufe wannam shafi kafin mu kawo sunayen su da lambobin su da hotunan su, domin duk muna da shi yanzu.
An Yi Nasarar Rufe Shafin
Daga Ali Imam Indabawa
Cikin Nasara da Taimakon Ubangiji mun samu Kawar da Tsinannen Page din nan me Suna Kasuwar Mata Mai dauke da Fans Kusan Dubu Arba'in wanda wasu 'yan Iskan Gari suka bude Suna Iskanci da Shashanci Wasu Mahaukatan Suna Biye musu, A Yanzu Haka babu wannan Page din A Dandalin Facebook, Muna Matukar Godiya Ga Allah bisa Wannan Nasara.
Madogara Rariya
Title :
An Rufe Shafin KASUWAR MATA A Facebook
Description : Hankali ya tashi matuka da bayyanar wani shafi mai suna kasuwar mata da wasu lalatattun matasa suka bude suna dauko hoton matan mutane suna...
Rating :
5