A ranar Litinin da misalin karfe 10 na dare ne wani dalibi mai suna Aminu Badamasi da aka fi sani da Justice mai kimanin shekara 28 da ke sashin Ilimin Zamantakewa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya rasa ransa a bayan da wani matashi mai suna Yusuf Abdullahi da aka fi sani da Mutuwa mai shekara 24 ya burma masa wuka a ciki lokacin da yake kokarin sulhunta wadansu kan bashin Naira 500.
Marigayin da wanda ake zargi da kashe shi suna zaune ne a Layin Sule Ajasko da ke Jushi kusa da Kwanar Maishanu a hanyar Jos a karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Yayan marigayin Balarabe Badamasi ya shaida wa wakilinmu cewa, “Da misalin karfe 10 na dare a ranar Litinin na fita domin in sa waya a caji sai na ga marigayi kanena da abokansa su uku suna hira sai muka gaisa na wuce. Na shiga shago ke nan sai na ji hayaniya ina fita aka ce ai an kashe Aminu kuma na hangi Yusuf Mutuwa rike da wuka an rasa mai zuwa. A haka na yi kunar bakin wake na fada masa na buge shi ya fadi jama’a suka zo suka kama shi. Bayan tabbatar da rasuwar kanina, sai matasa suka yi yunkurin kashe Yusuf Mutuwa amma muka hana su har ’yan sanda su zo su kama shi, mu kuma muka dauki gawar kanena muka kai gida shi ne aka yi jana’izarsa.”
Mahaifiyar marigayin Malama Zainab Mohammed cikin kuka ta ce danta ya samu kyakyawar shaida domi a kan kokarin da yake yi wajen sulhuntawa ne ake yi masa lakabi da Adalci kuma a kan haka Allah Ya karbi rayuwarsa.
daya daga cikin abokan marigayin wanda abin ya faru a idanunsa da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce, “Muna zaune sai muka ji ana jayayya tsakanin Aminu Mai Indomi a kan raguwar bashin kudin kwai Naira dari biyar da ya karba a hannun Dini Abdullahi tun cikin azumi bai biya ba. Shi ne shi marigayi Aminu ya taso domin ya sulhunta su kuma ya cire Naira 500 ya biya Dini, sannan ya yi musu nasiha. Shi Yusuf da ya yi kisa ba da shi ake yi ba, kuma ba abin da ya shafe shi a maganar. Kawai sai muka ga ya burma wa marigayi Aminu wuka a ciki ya kuma yiwo kan mutane.”
Wakilinmu ya ce bayan kammala jana’izar marigayin matasa daga makabarta dauke da makara sun wuce ofishin ’yan sanda suna cewa sai ’yan sanda sun ba su Yusuf Mutuwa su kashe shi tunda ya saba raunata mutane kuma ya taba kashe wani a Abuja ya gudo ga shi yanzu ya kara kisan kai, don haka a ba su shi su kashe shi su huta. Sai da ’yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa kafin su tarwatsa matasan.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu bayan sun kammala bincike za su gabatar da wanda ake zargi a gaban shari’a domin ya fuskanci hukunci.
Aminiya
Title :
An Kashe Dalibi Yana Kokarin Sulhunta Rikicin Naira 500
Description : A ranar Litinin da misalin karfe 10 na dare ne wani dalibi mai suna Aminu Badamasi da aka fi sani da Justice mai kimanin shekara 28 da ke s...
Rating :
5