An sanar da haramta nuna fina-finan ne a biranen Lahore da Karachi da kuma Islamabad.
Sun dauki matakin ne bayan dakarun sojin kasashen biyu sun soma tayar da jijiyoyin wuya a kan iyakar Kashmir.
A ranar Alhamis, kungiyar masu shirya fina-finan India ta Indian Motion Picture Producers Association, ta hana jaruman kasar Pakistan taka rawa a Bollywood.
Wani babban dan siyasar India mai ra'ayin kishin kasa ya umarci jaruman Pakistan da su fice daga kasar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin dakarun sojin kasashen biyu ke shafar sauran al'amuransu ba.
Title :
An Haramta Nuna Fina-finan India a Pakistan
Description : An sanar da haramta nuna fina-finan ne a biranen Lahore da Karachi da kuma Islamabad. Sun dauki matakin ne bayan dakarun sojin kasashen bi...
Rating :
5