Sanarwar ta fito ne daga Jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sandan jihar Katsina ASP Salisu Abubakar Agaisa. Wanda ya bayyana cewa duk wata kungiya ko wani da aka kama ya keta dokar zai hadu da fushin hukuma.
Haka ma rahotanni sun nuna cewa a jihar Kano ma an sanya doka makamancin haka. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Musa Magaji Majiya ne ya bayyanawa manema labarai hakan.