An soki lamirin shahararren dan wasan kwallon kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo bayan ya daura hotunansa a kafafen sadarwa inda ya daura kafa daya akan gunkin Buddha.
Hoton ya harzuka mabiya addinin Buddha inda suka dinga sukar dan wasan da munanan kalamai, inda har wasu ma suka ce sun janye goyon bayan da suke masa. Sa’annan suka bukaci ya cire hoton.
Tsananin ya sanya wasu daga cikin mabiya addinin suka dinga yi mai mugun fata, inda wasu suka yi mai addu’ar kwallonsa ta lalace.
Jama’a da dama suna ganin ubangijin Budha yafi karfin a wulakanta shi, saboda suna tunanin nasarar da kungiyar Leicester ta samu na lashe gasar Firimiya na bara yana da nasaba da goyon bayan da wasu shehunnan malaman addinin Buddha suka baiwa kungiyar.
Shehunnan malaman sun yi ma kungiyar addu’ar neman sa’a ne a wani gidan bautansu dake cike da gumakan addininin Buddha, inda mataimakin shugaban gidan Abbott Phra Prommangkalachan ya jagoranci wani addu’ar neman sa’a ga kungiyar.
Zaku iya duba wasannin da za’a buga a gasar Firimiya na kasar ingila tare da sakamakon wasannin.
source Naij hausa
Title :
An Caccaki Ronaldo Saboda Cin Mutuncin Addinin Buddha
Description : An soki lamirin shahararren dan wasan kwallon kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo bayan ya daura hotunansa a kafafen sadarwa inda ya daur...
Rating :
5