Fitaccen mawakin nan na Amurka, Akon, ya gayyaci Rahama Sadau zuwa birnin Los Angeles domin ya karfafa mata gwiwa bayan korar da aka yi mata daga Kannywood, kamar yadda majiyarmu ta BBC ta rawaito.
Shi ma shahararren mai shirya fina-finan Hollywood, Jeta Amata, ya gayyaci fitacciyar 'yar wasan zuwa Amurka domin ta taka rawa a fina-finan na Hollywood.
Mutanen biyu dai sun yi wannan gayyata ne a shafukansu na Twitter.
Ba wannan ne karon farko da take jawo ce-ce-ku-ce ba.
Akon, wanda cikakken sunansa shi ne Aliaume Damala Badara Akon Thiam, mawaki ne kuma jarumin fina-fina, wanda ya girma a kasar Senegal.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce "Ina shaukin haduwa da ke [Rahama) a LA [ Los Angeles]. Ya kamata mu karfafa gwiwar mata sanna mu taimaka musu domin su ci gaba. Zaunawa tare da su ya fi a yi watsi da su."
Shi kuwa Jeta Amata cewa ya yi, "Muna shirin tarbar daya daga cikinmu [Rahama] a Hollywood!"
An kori Rahama Sadau daga Kannywood ne saboda rungumar da ta yi wa wani mawaki mai suna Classiq a bidiyon wakar da ya sanya ta a ciki.
Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa ta nemi gafara, kodayake ta ce abin da ta yi din "ba laifi ba ne" a tsarin sana'arta
Title :
Akon Ya Gayyaci Rahma Sadau Kasar Amurka Domin Karfafa Mata Gwuiwa
Description : Fitaccen mawakin nan na Amurka, Akon, ya gayyaci Rahama Sadau zuwa birnin Los Angeles domin ya karfafa mata gwiwa bayan korar da aka yi mat...
Rating :
5