Wani mutumi mai shekaru 40 a duniya, Hafisu Ishaku ya yi ma yar cikinsa mai shekaru 13 ciki. Ishku yayi ikirarin cewa ya yi abun ne don asiri amma matarsa bata amince ba.
Mutanen Kabala Doki, karamar hukumar Kaduna North, Matar Ishaku wacce aka kira da suna Maryam ta bayyana wa kotu cewan Hafizu yayi ma yarsu ciki yayinda tayi tafiya ganin iyayenta na watanni uku.
Ta ce: “Lokacin da na dawo daga ganin iyayena, na lura da canji dangane da yata a matsayina na uw, bata da kuzari kamar da a lokaci guda kuma tana rashin lafiya. Amma banyi zargin komai ba da farko saboda mijina yana bata wasu hade-hade ta sha a koda yaushe wanda yake ikirarin cewa shi zai magance ciwon dake damun yarmu.”
“Amma ciwon yaki ci yaki cinyewa kuma na lura cewa yata tayi batan wata, na tilasta mata sai ta fada mun. tace mun mahaifinta ne yayi mata ciki a lokacin da nayi tafiya. Don haka lokacin da na tunkari Hafizu, yayi kuka ya fadi gaskiyan cewa ya shiga kungiyar asiri wanda suka tilasta shi yayi ma yarsa ciki ya kuma zubar dashi a matsayin hadaya.”
Ta kara da cewa “Amma bayan an zubar da cikin sai na lura da cewa mahaifin nata ya ci gaba da jima;I da yar tasu.”
A cewar jaridar Daily Sun, ba’a samu jin ta bakin Hafizu wanda ke siyar da kayan wuta a kasuwar Maraba Abuja ba a lokacin da ake hada wannan rahoto.
naij Hausa
Title :
Abin Kunya: Uba Yayi Ma Yarsa Ciki A Jihar Kaduna
Description : Wani mutumi mai shekaru 40 a duniya, Hafisu Ishaku ya yi ma yar cikinsa mai shekaru 13 ciki. Ishku yayi ikirarin cewa ya yi abun ne don asir...
Rating :
5