Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a cikin raha yake lokacin da ya ce dafa abinci ne aikin matarsa, bayan zazzafar hirar da aka yi da ita a BBC, inda ta caccaki yadda gwamnatinsa ke tafiya.
Kalaman da Buhari ya yi a Jamus cewa aikin matarsa shi ne "dafa abinci, kula da falo da kuma daki" ya jawo suka daga mutane da dama musamman mata.
"Dole ne a siyasa sai an hada da raha domin a kara mata armashi", a cewar mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu.
Ya kara da cewa "Mu da muke kusa da shi mun san cewa ba ya rabo da raha".
Shugaba Buhari ya kara da cewa yana mutunta matsayin mata a cikin al'umma.
Ya ce hakan ne ma ya sa ya nada mace Kemi Adeosun (ministar kudi), akan daya daga cikin mukaman da suka fi kowanne muhimmanci a gwamnatinsa.
....Hirar BBC da Aisha Buhari ta tayar da kura
Ita dai uwargidan shugaban, Aisha Buhari, ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.
"Bai gaya min cewa zai tsaya ko ba zai tsaya ba tukunna, amma na yanke shawara a matsayina na matarsa, cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, to ba zan shiga cikin tafiyar ba.
"Idan har abubuwa ba su sauya ba, to ba zan fita na yi yakin neman zabe kamar yadda na yi a baya ba. Ba zan sake yi ba".
Rariya
Title :
A Cikin Raha Na Maidawa Matata Martani, Inji Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a cikin raha yake lokacin da ya ce dafa abinci ne aikin matarsa, bayan zazzafar hirar da aka yi da ita a BBC,...
Rating :
5