Gwamnatin jihar Imo ta kaddamar da wani shiri na yin afuwa ga wasu daga cikin matasan Naija Delta masu gwagwarmaya da makamai, bayan ajiye makaman nasu. Matasan wadanda sun kai kimanin dubu uku sun fito daga yankunan kananan hukumomi biyu masu albarkatun man fetur, a jihar.
Matasan dai, kamar takwarorinsu na sauran yankin Naija Delta, ana zargin su da zama wata babbar matsala ga sha'anin tsaro da aikin hakar mai. Gwamnatin jihar ta ce matasan sun mika makamai da dama da suke amfani da su wajen lalata bututan mai.
Gwamnatin dai ta ce nan gaba za ta bi wani tsari da zai sanya matasan su cuɗanya da sauran mutanen gari. Wasu daga cikin matasan sun ce buris da gwamnati ta yi da yankunansu ne ya sanya su daukar makamai, a baya.
Rariya
Title :
Za A Yi Afuwa Da Tsagerun Niger Delta Sama Da Dubu Uku
Description : Gwamnatin jihar Imo ta kaddamar da wani shiri na yin afuwa ga wasu daga cikin matasan Naija Delta masu gwagwarmaya da makamai, bayan ajiye ...
Rating :
5